Nigeria ta ce akwai wahala da kwana-kwana tattaunawa da BH

Nijeriya Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Nijeriya ta ci alwashin ganin an sako karin wasu 'yan matan Chibok daga hannun 'yan Boko Haram

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta hau teburin ci gaba da tattaunawa da Boko Haram don ganin an sako sauran 'yan matan sakandaren Chibok da har yanzu ke hannun ƙungiyar Boko Haram.

Gwamnatin ta kuma bayyana tabbacin cewa tattaunawar za ta haifar da sakamako mai kyau nan gaba kaɗan.

A ranar Juma'a ce 14 ga watan Afrilu, 'yan matan sakandaren Chibok kimanin 200 ke cika shekara uku a hannun ƙungiyar Boko Haram.

Kakakin fadar shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu ya faɗa wa BBC cewa "Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ƙarfafa gwiwar cewa a nan kuma ana tattaunawa ta wasu hanyoyi daban-daban... don ganin an samu karɓo ƙarin wasu 'yan mata(n Chibok) a kan waɗanda aka samu a da."

Ya ce ana yin tattaunawar ce da taimakon wasu ƙasashen waje. A cewarsa "Kuma ka san ko waɗancan 'yan mata 21 da aka samu aka karɓa ka san akwai sa hannun Ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross, akwai kuma jami'ai na gwamnatin Switzerlands," ya ce har yanzu ba su janye hannu a cikin tattaunawar ba.

Garba Shehu ya kuma ce " Akwai ma (ƙarin) wasu ƙasashen su ma da aka samu haɗin kansu ana tattaunawar da su."

Gwamnatin Nijeriya ta dai ce ana wannan tattaunawa ce a daidai lokacin da dakarun sojin ƙasar ke ci gaba da ƙoƙarin kakkaɓe mayaƙn Boko Haram a dajin Sambisa.

Asalin hoton, Nigeria government

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka sako a baya tare da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari

Da aka tambaye shi ko me ya sa shekara uku bayan sace 'yan matan sakandaren Chibok amma har yanzu gwamnati ba ta iya kuɓutar da su ba? Garba Shehu Ya ce babbar matsalar ita ce gwamnati ba ta san inda 'yan matan suke ba.

"Yau inda an san inda suke ai ina ce maka awa 24 ta yi yawa, dakaru da jami'an tsaro za su iya shiga ko ina a ƙasar nan su kuɓutar da su."

A cewarsa duka ɓangarorin Boko Haram na zuwa teburin tattaunawa da gwamnatin Nijeriya ta hanyar masu shiga tsakani..

''Tattaunawa irin wannan tana da wahala, tana da kwane-kwane tana da murɗiya, abu ne da ko an so a yi garaje ba lallai ne ta tafi a haka ba, saboda haka tana buƙatar dauriya da haƙuri,'' in ji shi

A watan Oktobar shekara ta 2016 ne aka sako 'yan matan Chibok 21, bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin Nijeriyar da Boko Haram, tare da shiga tsakanin gwamnatin Switzerland da kungiyar agaji ta Red Cross.