'Tare wa motocin shugaban ƙasa hanya cin amanar ƙasa ne'

Zambia's Opposition leader Convoy
Bayanan hoto,

Shugaban 'yan adawar na tafiya da kwambar motocinsa lokacin da shugaban Zambia ya zo wucewa

An tuhumi jagoran 'yan adawar Zambia Hakainde Hichilema da cin amanar ƙasa bayan ya tarewa kwambar motocin shugaban ƙasa hanya.

Ɗan adawar wanda ke tafiya da kwambar motocinsa ya ƙi ratsewa a gefe don motocin shugaba Edgar Lungu su wuce a ranar Lahadi.

Hayaniya ta ɓarke a lokacin da kwambar motocin shugaban ta yi ƙoƙarin shige na Hichilema.

Babu wanda ya ce uffan tsakanin Hakainde Hichilema ko lauyansa tun bayan tuhumarsa.

Bayanan hoto,

Sai da ƙura ta tashi sama a lokacin dafdalar kwambar motocin

'Yan sanda sun ce kwambar motocin Hakainde Hichilema ta sanya rayuwar shugaban ƙasa cikin hatsari.

Cin amanar ƙasa tuhuma ce da ba a bayar da beli a Zambia, kuma ana iya ɗaure mutum mafi ƙaranci shekara 15 ko kuma ma hukuncin kisa.

A ranar Talata ce 'yan sanda ɗauke da makamai suka kama jagoran 'yan adawar a gidansa da ke Lusaka babban birnin ƙasar.

Ya zargi 'yan sanda da harba hayaƙi mai sa hawaye a gidansa a lokacin da uwargidansa, Mutinta Hichilema, ke cewa suna "son kashe mini miji".

A bara ne, shugaba Lungu ya kayar da Mr Hichilema da ɗan ƙaramin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hakainde Hichilema ya ce an yi masa ƙwace a lokacin zaɓen shugaban ƙasar na bara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Su dai 'yan adawa na zargin shugaba Lungu da ƙoƙarin yi musu ƙanshin mutuwa

Jam'iyyar UNPD ta Hichilema ta ce ba ta amince da Lungu a matsayin shugaba Zambia ba, bayan ta yi zargin tafka maguɗi.

An tuhumi jagoran adawar tare da wasu mashawartansa su biyar, bayan tseren motocin da suka yi a kan titin zuwa Mongus daga Limulunga.

Babban jami'in 'yan sanda Kakoma Kanganja ya faɗa wa manema labarai cewa "Jagoran adawar ya ƙi bin umarnin 'yan sanda na bai wa kwambar motocin shugaban ƙasa hanya a yunƙurinsa na sanya rayuwar shugaban Zambia a hatsari."

Da ma dai Hichilema na fuskantar tuhume-tuhume a kan tunzura jama'a su yi bore tun a watan Oktoban bara, matakin da jam'iyyarsa ta ce yunƙuri ne na rufe masa baki.