Mu ma ba mu san inda 'yan Chiɓok suke ba —Burtaniya

Chibok girl's parents
Bayanan hoto,

Har yanzu iyayen 'yan matan Chiɓok na da sauran fatan za a ceto 'ya'yan nasu

Jakadan Burtaniya a Nijeriya, Paul Thomas Arkwright ya ce ƙasarsa ba za ta tura sojoji ko ta ƙaddamar da samame a dajin Sambisa don ganin an sako 'yan matan Chibok ba.

Ya ce ba za su iya samar da haƙiƙanin bayani a kan taƙamaiman inda ake tsare da 'yan matan makarantar sakandaren Chiɓok ba.

A cewarsa ba abu ne mai sauƙi ba sanin inda ɗaukacin 'yan matan suke a daidai lokacin da ake cika shekara uku da sace su ranar 14 ga watan Afrilun 2014.

Jakadan ya ce sai dai za su ci gaba da samar da bayanan sirri da aiki tare da gwamnatin Nijeriya don gano inda 'yan matan na Chiɓok suke.

"Aikin sojin Nijeriya ne ceto 'yan matan sakandaren Chiɓok, mu sai dai mu tallafa musu kawai," in ji Arkwright.

Ya ce ba shakka a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, Burtaniya da sauran ƙasashen duniya sun yi tayin tallafawa.

Ya ce suna bai wa Nijeriya bayanan sirri da kuma tallafa wa gwamnati har yanzu don kuɓutar da 'yan matan.

Ya ce a 2016, Burtaniya ta horas da sojan Nijeriya sama da dubu 22 don zuwa su tunkari Boko Haram.

Arkwright ya ce suna samun kyakkyawan haɗin kai ta fuskar aikin soja da kuma bai wa jami'an Burtaniya damar kai ziyara zuwa yankin arewa maso gabas.