'Ba ɗan sanda ne kaɗai zai shugabanci EFCC ba'

Senate

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE

Bayanan hoto,

Ɓangaren zartarwar Nijeriya da majalisar dattijai sun samu saɓani a kan naɗin shugaban EFCC Ibrahim Magu

Majalisar wakilan Nijeriya ta fara yi wa dokokin da suka kafa hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa gyara.

Matakin dai wani yunƙuri ne na inganta ayyukan hukumar wadda aka kafa dokokinta a shekara ta 2004 don ƙara zaburar da ita.

A cewar shugaban kwamitin harkokinn yaɗa labarai na majalisar, Abdurrahman Namdaz ya ce gyaran fuskar da za a yi wa hukumar ta EFCC za su shafi manyan sassa guda uku ne.

Ya ce dokar da ta kafa hukumar, na son ganin sashen leƙen asirin harkokin kuɗi na EFCC (Financial Intelligence Unit) yana cin gashin kansa, saɓanin yadda abin yake a yanzu.

"A yanzu haka shugaban hukumar EFCC ne yake lura da wannan sashe (maimakon ya kasance mai cin gashin kansa)."

Haka zalika, majalisa za ta gyara doka ta yadda ba lallai ne sai ɗan sanda ko wani jami'in tsaro kaɗai za su iya shugabantar EFCC ba, in ji Namdaz.

Tun bayan kafa hukumar a zamanin mulki shugaba Olusegun Obasanjo, 'yan sanda ne suke shugabanci a hukumar mai yaƙi da cin hanci.

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Tun da aka kafa hukumar ta EFCC a Nijeriya 'yan sanda ne kamar Ibrahim Magu ke shugabancinta

A yanzu dai jami'in 'yan sanda ne, Ibrahim Magu ke shugabancin EFCC kuma ana ganin ba shi da farin jini a wajen 'yan majalisun ƙasar.

Sau biyu majalisar dattijai ta Nijeriya na yin watsi da sunan Magu lokacin da fadar shugaban ƙasar ta gabatar da shi don tabbatar da masa da shugabancin EFCC.

A cewar Namdaz, za kuma su gyara sashen da ke cewa idan hukumar ta ƙwace dukiyar da wani ya yi almundahana da ita, a mayar wa gwamnatin tarayya ita.

Ya ce "Mun fahimci cewa wasu kayan da (EFCC) kan yi bincike a kansu, mallakar gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi ne, don haka muna ganin ya kamata a gyara ta yadda za a mayarwa mai dukiya, haƙƙinsa."

Ɗan majalisar ya ce ƙudurin gyaran fuskar yana fuskantar karatu na biyu a zauren majalisar wakilai don haka akwai ƙarin batutuwan da ka iya shiga cikin garambawul ɗin da za a yi wa EFCC.