An tilasta wa jam'iyyu nuna fuskar 'yan takara mata a Algeria

poster Hakkin mallakar hoto Hizb al adal wal bayan
Image caption Wasu jam'iyyu sun boye fuskokin 'yan takaransu mata

Jam'iyyun siyasa a kasar Aljeriya sun amince su bayyana fuskokin mata 'yan takara bayan sun boye fuskokinsu a takardun tallata 'yan takara wato fosta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana.

Wasu jam'iyyu a lardin Bordj Bou Arreridj sun sanya hoton hijabi a gurbin 'yan takara mata, sai kuma su sanya hotunan sauran 'yan takara maza tare da bayyana fuskokinsu.

A ranar Talata ne hukumar zaben kasar ta bai wa jam'iyyun wa'adin kwana biyu, inda ta ba su zabi biyu wato su bayyana fuskokin 'yan takara mata, ko kuma su janye su daga yin takarar.

Wani jami'i ya ce boye fuskar 'yan takara ya saba wa doka.

"Irin wannan wuce gona da iri yana da hadari sosai, ya saba wa doka hakazalika al'ada," in ji wani mai sa ido a zabe, Hassan Noui.

Ya ci gaba da cewa "Hakkin jama'a ne su san wanda za su zaba."

Daga nan, sai ya ce akwai akalla jam'iyyu biyar da ba sa bayyana fuskokin 'yan takararsu mata a jikin takardun tallata 'yan takara.

Kin bayyana fuskokin 'yan takara mata ya jawo muhawara a kasar.

Wata 'yar takara mai suna Fatma Tirbakh ta jam'iyyar (NFSJ) da ke gabashin lardin Ouargla ta ki bayyana fuskarta yayin da take magana ta gidan wani talabijin da ke kasar.

"Na yi amannar cewa bayyana hotona abu da yake da muhimmanci, amma na fito ne daga kudancin kasar. Maganar gaskiya wuri ne na masu tsatstsauran ra'ayi saboda haka ne aka ki bayyana hotona," in ji ta.

An wajabta wa jam'iyyun kasar tsayar da mata 'yan takara a karkashin wata doka da ta bukaci ware wa mata kaso 20 zuwa 50 cikin 100 na tikitin takara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aljeriya za ta yi zaben majalisar dokoki a ranar 4 ga watan Mayu

Wani jami'in jam'iyyar Socialist Forces Front (FFS) Hassen Ferli ya dora alhakin boye fuskokin 'yan takarar a lardin Bordj Bou Arreridj ga kwamitin yada labaran jam'iyyar, inda ya bayyana lamarin da "abin takaici."

Ya ci gaba da cewa "Jam'iyyar FFS ta yi Allah-wadai da lamarin wanda ya ci karo da manufofin jam'iyyar."

Har ila yau, ya ce jam'iyyar ta dukufa wajen kawo daidaito tsakanin maza da mata.

Aljeriya ba ita kadai ce kasar da ake boye fuskokin mata da ke takarar neman kujerar majalisar dokoki ba a cikin takardun tallata 'yan takara.

Don ko lokacin zaben majalisar dokokin Masar na shekarar 2011 zuwa 2012, jam'iyyar Salaf ta yi amfani ne da hoton fure a madadin hotunan 'yan takaranta mata.

A shekarar 2012 jam'iyyun masu kishin Islama na Salafist sun yi amfani da firanne maimakon hotunan mata 'yan takara a zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Masar.

Labarai masu alaka