'Rasha ta gaza kare kisan kiyashi a makaranta a Beslan'

Kotun Kare Hakkin dan Adam ta Turai ta ce Rasha ta gaza wajen hana faruwar kawanyar da aka yi wa wata makaranta a garin Beslan a shekarar 2004, inda fiye da mutum 330 suka rasa rayukansu.

Hakazalika, binciken da aka gudanar ya soki samamen da aka yi don kawo karshen kawanyar da kuma irin makaman da aka yi amfani da su.

A lokacin kawanyar, 'yan awaren Chechnya sun yi garkuwa da fiye da mutum dubu wadanda galibinsu yara ne.

Lamarin ya zo karshe ne bayan da dakarun Rasha suka kai farmaki a kan ginin makarantar. Wasu da suka tsira daga al'amarin sun ce dakarun sun yi amfani da karfi fiye da kima.

Sai dai ba wani jami'in Rasha da aka kama da laifi kan kisan dumbin mutane, ciki har da yara 186.

Mene ne ya faru a garin Beslan a lokacin?

Wasu mutane maza da mata, wadanda suka rufe fuskokinsu kuma suka yi damara da bama-bamai, sun kutsa kai cikin wata makaranta inda suka bude wuta a daidai lokacin da ake bikin fara sabon zangon karatu.

Maharan sun cunkusa wadanda suka yi garkuwa da su a wani zauren wasannin kwallon kwandon makarantar, inda suka rika jefa musu nakiyoyi. Bukatar maharan dai ita ce dakarun Rasha su janye daga yankin Chechnya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An tara wadanda aka yi garkuwa da su a zauren wasannin makarantar

Kawanyar ta zo karshe ne a rana ta uku bayan fashewar wasu manyan bama-bamai biyu da kuma musayar wuta. Wadanda suka shaida al'amarin sun bayyana farmakin da dakarun Rasha suka kai a matsayin wani abu mai tayar da hankali, inda suka ce dakarun sun yi amfani da manyan makamai da kuma karfi da ya wuce kima.

Mutum guda ne daga cikin maharan ya tsira da ransa kuma an gurfanar da shi a gaban kuliya.

Mene ne abin da wadanda suka tsira daga harin da kuma danginsu ke cewa?

Fiye da shekara 10 yanzu, wadanda suka tsira da danginsu suna cewa watakila za a iya kaucewa kawanyar kuma kila da mutane da dama ba su mutu ba lokacin a kokarin kubutar da su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kai farmaki a makarantar ne a ranar farko ta sabon zagon karatu

Sun ce mahukunta, ciki har Shugaba Vladimir Putin, ba su yi abin da ya dace ba game da al'amarin garkuwa da mutanen. Har ila yau, akwai batun da ke cewa ba su yi aiki da bayanan sirrin da suke cewa an kitsa al'amarin ne tun da farko.

Rasha ta fara wani bincike kan al'amarin, amma kuma an dakatar da shi tun a shekarun baya.

Hakan ya sa fiye da mutum 400 da abin ya shafa suka kai kokensu gaban Kotun Kare Hakkin dan Adam ta Turai.

Wane hukuncin kotun ta yanke?

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fiye da yara 180 suka mutu a yayin kawanyar

Kotun da take birnin Strasbourg na kasar Faransa ta yanke hukuncin ne ta hanyar Hukumar Turai, wadda Rasha take matsayin mamba.

Hukumar ta bambanta sauran hukumomin Turai kuma ba reshe ce ta Tarayyar Turai ba. Aikinta shi ne kare hakkokin mazauna nahiyar.

Ta ce Rasha tana da bayanan da ke nuni da cewa an kitsa kawo hari a wurin, amma sai ta ki yin wani abu don kaucewa faruwarsa.

Har ila yau, ta ce "manyan makamai kamarsu manyan bindigogi da ake harba su daga kan ikwa da bindigar harba gurneti, an yi amfani da su a makarantar wanda hakan ya jawo mummunar asara.

Wajibi kasashe su yi amfani da hukuncin kotun, ko da yake kotun ba za ta iya tilasta hakan ba.