Har yanzu 'yan Chibok suna raina — Buhari

Chibok

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zuwa yanzu an gano 'yan matan 24

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da tattaunawa da 'yan Boko Haram don ganin an 'yanto sauran 'yan matan Chibok da sauran mutanen da suke rike da su cikin koshin lafiya.

Ya ce: "Ta hanyar masu shiga tsakani a ciki da wajen Najeriya, za mu yi dukkan mai yiwu wa don tabbatar da cewa dukkan sauran 'yan matan sun kubuta".

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kwana guda gabanin cika shekara uku da sace 'yan matan fiye da 200 daga makarantar sakandaren Chibok.

Har ila yau, ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen bai wa dakarun kasar da sauran jami'an tsaro goyon bayan da ya dace a kokarin ganin an dawo da 'yan matan da kuma kwato yankunan da 'yan Boko Haram suke ci gaba da iko da su. Ya ce hakan ne ya sa suka iya fatattakar 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa.

Daga nan ya ja hankalin 'yan Najeriya da sauran kasashen duniya kan kowa ya taimaka wajen yaki da ta'addanci "musamman idan aka yi la'akari da yadda matsalar ta shafi kowa da kowa". Hakazalika, ya yi kira ga 'yan kasar da su "rika kula sosai don kai rahoton duk wani abu da ba su gane masa ba."

A sanarwar da shugaban ya fitar ranar Alhamis, ya kara da cewa, "Ya kamata mu yi farin ciki da kubutar da 24 daga cikin 'yan matan da aka yi da kuma sauran 'yan Najeriya da aka kwato su daga hannun 'yan ta'addan."

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin ganin 'yan matan da suka kubuta sun koma cikin al'umma suna tafiyar da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

"Ina mika godiyata ga iyayen yaran nan da iyalansu, wadanda suka jure takaici da fargaba na tsawon shekara uku suna jiran dawowar 'ya'yansu. Ina jin duk abin da ku ke ji. 'Ya'yanku nawa ne. Don haka a wannan rana ina kiran ku da ka da mu karaya wajen fatan dawowar sauran 'yan matan nan.," in ji shugaba Buhari.

Ranar 14 ga watan Afirulun 2014 ce aka sace wadannan 'yan mata fiye da 200 daga makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.