Kun san yadda ake auratayya tsakanin Kirista da Musulmi a Masar?

Masar
Bayanan hoto,

Misis Sally ta yi kwalliya a ranar aurenta

Hare-haren da aka kai cocin Kifdawa a arewacin Masar wannan mako na jaddada irin hadarin da Kiristoci marasa rinjaye a kasar ke fuskanta.

Amma a tsakanin 'yan kabilar Nubia, al'ummar da ke zama a gabar kogin Nile, Musulmai da Kirista na zaman lafiya.

Nicola Kelly ta halarci bikin aure tsakanin Musulmi da Kirista a kudancin birnin Aswan, wanda aka yi da dare.

Akram ya ce ''Kowa na ce min kamata ya yi na auri wata daga al'ummarmu amma ya gagara. Ba zan iya zama ba tare da ita ba.''

Safiyar ranar auren Akram ne, a wani kauye da ke gabar Nile, ya shirya domin zuwa masallaci domin a daura aure.

Wannan bikin ba na gargajiya ba ne. Mista Akram shi kadai zai je wurin daurin auren, yayin da amaryarsa Misis Sally wacce Kirista ce za ta yi adduo'inta a gida.

Mista Akram ya ce ''Mu ne mutane na farko da suka yi aure ba bisa ka'idojin addininmu ba. Lamari ne mai wuya sosai, musamman ma ga iyayena.

Iyayen ma'auratan sun hana su ganawa da juna tsawon shekara bakwai.

'Yan al'ummar da shugabannin addini da kuma abokansu, sun yi kokarin hana su ganawa da juna, amma sun kirkiro wata dabara don yin hakan.

Mista Akram ya ce'' Mun amince mu daura aure da dare, domin kada mu jawowa danginmu abin kunya.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gabar Kogin Nile da za'a daura auren

Ba a haramta aure ga ma'aurata kamar Misis Sally da Mista Akram, masu addini dadan-daban ba amma an haramta yinshi cikin jama'a.

Don haka, ma'aurantan na shagalin bikin daban-daban, har sai dare, sai su hadu a kebabben wuri su cika sharuddan aurensu.

Mista Akram da Misis Sally sun hadu ne shekaru bakwai da suka gabata a Aswan da ke gabashin gabar Nile, inda matasa ke haduwa, su sha askrim.

Wurin ba shi da nisa da kauyensu, Shadeed.

A wasu wuraren a Masar, auren Mista Akram da Misis Sally zai kasance mai hadari.

Tun lokacin juyin-juya hali na shekara 2011, hare-haren da ake kai wa kan Kirista ya karu.

A shekarar da ta gabata an kai hare-hare 54 kan 'yan addinin kirista marasa rinjaye da kuma harin kunar bakin wake da aka kai wa cocin Kifdawa da ke Alkahira kafin Kirismeti.

A farkon wannan makon ne aka kashe mutum 45 kuma wasu da dama suka ji rauni a lokacin da aka kai hare-hare biyu a cocin Kifdawa a Alexandria da na birnin Tanta da ke kusa da Nile Delta.

Amma Mista Akram bai damu ba

A makon da ya gabata , zance daya Akram yake yi, yana bi gida gida domin gayyatar mutane zuwa aurenshi. Wannan al'ada ce ta 'yan kabilar Nubia. A al'adarsu tamkar ka zagi mutum ne idan ka tura masa katin gayyata maimakon ka je gida ka gaya mai.

Bayanan hoto,

Akram wanda ke tsakiya na zuwa gida gida domin ya gayyace abokanshi zuwa aurenshi

A al'ummarmu saki ba abu ne da aka saba yi ba. Kuma ba a yarda da auren sama da mace daya ba. Ga maza matasan al'ummar, addini kirista yayi matukar tasiri garesu.

Bayanan hoto,

Sally a safiyar ranar aurenta

" Kawai abinda ya kamace ni, shi ne na fito na yi rawa kuma mutane su yi min murna sai kuma mu tafi, kamar yadda Sally ta fada cike da annushuwa.

Bayanan hoto,

Sally ta sha lalle a hannayenta

Da dare ya fara karatowa sai matan suka shiga kwale-kwale domin suje su yi gyaran gashinsu. Ita ma Sally ta nufi gidan gyaran gashin.

Bayan 'yan sa'oi kadan, sai Sally ta dawo ta sha kwaliyya ba kamar yadda take da farko ba.

"Yanzu cike nake da kuzari, nasan yanzu na yi kyau.

Da karfe 12 na dare sai ga motar ango bayan an shafe tsawon lokaci ana jira.

"Ya makara , Sally ta fadawa kawayenta cikin fushi tana ihu.

A waje kuma Akram yana ta gyara nakatayi da ya daura a wuyanshi yana kuma gyara gashinshi.

"Wanan ne karon farko da na saka kwat . Sam bana jin dadinshi a jikina, na matsu na cire su na saka jallabiya na bayan an kammala rawan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Da farko mata da maza ba su yin rawar tare.

Kawayen amaryar suna kewaye ta ne domin su tabbatar rigar da ta saka ba za ta tade ta ba.

A kusa da su kuma 'yan unwa da abokan arzikin Akram ne suke jefa shi sama a yayinda ake kida.

"Akram yayi ihu cikin annashuwa ya ce wannan ne lokacin da nafi so.

A wannan lokaci kuma, sai kawaye da abokai su bai wa amrya da ango wuri domin su yi rawa. Za su yi rawa tare amma kuma ba tare da sun rike junansu ba.

Bayan mintuna biyar, sai aka dakatar da kidan sannan sai amarya da ango su fara kallon juna cike da shauki.

Cikin farin cikin Akram ya ce "Yanzu za mu iya komawa Shadeed, mu ci abinci mu fara rayuwarmu tare.

Sai Sally ta yi murmushi cike da kunya a lokacin da take tsaye kusa da shi. Na tambaye ta ko ta matsu su fara rayuwa tare da angonta?

"Kwarai kuwa, na shirya fara haihuwa. Ta ce ina son yara dayawa a yayinda ta dan saci kallon mijinta. Ina fata kowa zai amince da aurenmu kuma zamu zauna lafiya.