Amurka ta jefa ƙaton bam kan 'yan IS a Afghanistan

Wannan ne karon farko da aka yi amfani da ban din

Asalin hoton, USAF/Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne karon farko da aka yi amfani da ban din

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ta jefa wani katon bam kan wani kogo da mayakan kungiyar IS suke buya a kasar Afghanistan.

Wannan shi ne karon farko da Amurka ke jefa wannan babban bam din, tun bayan gwajin da ta yi masa a shekarar 2003.

Ma'aikatar tsaron ta ce wani jirgin samanta ne ya harba bam din a lardin Nangarhar inda mayakan IS suke.

Amurka ta dauki wannan mataki ne sa'o'i kadan bayan ma'aikatar tsaron kasar ta amince cewa ta kai hari ta sama bisa kuskure a Syria wanda ya yi sanadin mutuwar masu tayar da kayar baya 18.

Ta ce dakarun tsaron da take hadin gwiwa da su sun yi kuskuren gano inda mayakan IS suke, lamarin da ya sa suka kai harin ranar 11 ga watan Afrilu kan masu tayar da kayar baya na the Syrian Democratic Forces, wadanda Amurka ke mara wa baya.

An kai hari a Afghanistan ne bayan wani sojan Amurka ya mutu a makon jiya a fafatawar da jami'an tsaro na musamman na kasar suka yi da mayakan IS a lardin Nangarhar.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an jefa bam din mai nauyin kilo gram 9,800 ranar Alhamis da yamma.

Kakakin fadar White House Sean Spicer, "Mun hari hanyar karkashin kasa da kogunan da mayakan ISIS ke amfani da su wurin yin zirga-zirga ba tare da shamaki ba, abin da ke sanya wa suna kai hari kan masu bai wa sojojin Amurka shawara kan tsaro da dakarun tsaron Afghanistan da ke yankin."

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Nato ta yi kiyasin cewa akwai mayakan IS tsakanin 1,000 zuwa 1,500 a Afghanistan