'Yan ci-rani kimanin 90 sun nutse a Tekun Libya

Wani dan ci-rani da ya tsira daga nutsewa a tekun Libya
Bayanan hoto,

Mohamed Amine na cikin wadanda suka tsira da ransu kuma aka kai su cibiyar Maitiga a birnin Tripoli da ake tsare 'yan ci-rani

Mutane sama da 90 ne ciki har da mata da ƙananan yara suka mutu bayan nutsewar kwale-kwalensu a kan hanyar tsallaka teku zuwa nahiyar Turai daga Libya.

An dai yi nasarar kuɓutar da 'yan ci-rani 23, yayin da wasu kuma ba a iya gano su ba.

Wadanda suka tsira da ransu sun ce kwale-kwalen da suke tafiya a cikinsa ba shi da ƙwari kuma ya ɗauko mutum 120, akasari daga yankin kudu da Saharar Afirka, don neman rayuwa mai kyau a Turai.

An ci gaba da aikin ceto, yayin da wasu rahotanni an fara yanke ƙaunar samun ƙarin wadanda ke da sauran numfashi.

Kasar Libya, wata babbar mashigar Turai ce 'yan ci-ranin da kan tsallaka Tekun Bahar Rum a jiragen kwale-kwale.

Mutum aƙalla 590 ne suka hallaka ko kuma suka ɓata a tekun Libya cikin wannan shekarar kaɗai, kamar yadda hukumar kula da ƙaura ta duniya ta ruwaito.

Wadanda suka tsira sun ba da rahoton cewa hatsarin ya faru ne bayan jirginsu ya huje, inda ruwa ya cika shi har ya dulmiye a tsakiyar teku.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kwale-kwalen 'yan ci-rani da dama sun nutse cikin teku a shekarun baya bayan nan

'Yan ci-rani kusan dubu 25 ne suka isa Turai tun farkon wannan shekara, a wani bulaguro mai cike da hatsari ta tekun Bahar Rum.

Suna tsallakawa ne ta ƙasar Libya wadda ita hanya mafi sauƙi, kuma mafi hatsari sakamakon rikicin da kasar ke fuskanta tun bayan hamɓare gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011.

Wani yaro mai shekara 12 da ke da sauran kwana wanda ya fito daga Ivory Coast - yanzu an ba shi wurin zama a cibiyar Maitiga a birnin Tripoli na kasar Libya, ya kuma shaida wa BBC cewa:

" jirgin ya tsage, kuma mahaifiyata ta halaka.''

Wani wanda ya tsira Mohamed Amine daga ƙasar Mali, ya ce "Muna cikin teku tsawon kwana uku. An ceto mu bayan kwale-kwalenmu ya jirkice.''