'Ko kusa da sakandarenmu ta Chibok ba na son zuwa'

Hauwa ta ce ranta yakan sosu duk lokacin da ta je kusa da makarantarsu
Wata 'yar makarantar sakandaren Chibok, Hauwa Lawan Zanna ta ce sace ƙawayenta da 'yan Boko Haram suka yi, ya sa ba ta ƙaunar ko wucewa ta kusa da makarantar a yanzu.
Yayin da take zagayawa da wakilin BBC Ibrahim Isah rusasshen ginin makarantarsu, ta tuna ƙanwarta Aisha Lawan Zanna da ƙawayenta Sara'atu John da Hadiza Abdullahi da Kabuh Mala da Aishatu Lawan da har yanzu ke hannun ƙungiyar Boko Haram.
Ƙawayen Hauwa na daga cikin 'yan mata sama da 200 da mayaƙan Boko Haram suka sace shekara uku da ta wuce.
Ta ce "Ni, Allah ya tserar da ni saboda a ranar ba mu da jarrabawa, don haka ina gida ban taho makaranta ba."
Hauwa wadda ƙwalla ta cicciko a idanunta, shugabar ɗalibai ce a ɗakinsu da ke karatun kimiyya, ta ce "Tabbas (har yanzu) muna sa ran(dawowarsu gida) domin komai ƙaddara ce."
Ta tuna filin wasanninsu na ƙwallo da ƙawayenta irinsu Sarayah John da Aisha Ababakar. "Yarinyar ƙarfi gare ta, im ma ta zo shan gaban mutum da bol. Har a ciki ta taɓa buga min.
Ta ce suna fama da baƙin ciki a rayuwa. Duk da haka ta ce suna roƙon Allah ya dawo da 'yan'uwansu gida.
Ta bayyana damuwa kan yadda aikin sake gina makarantar ya tsaya kimanin wata huɗu da ya wuce.
Aikin sake gina sakandaren Chibok ya tsaya
Bulollukan sake gina sakandaren Chibok yashe a gefen hanya
Hauwa ta ce "Ban san me ya faru (aka dakatar da aikin ba), ya kamata gwamnati ta ci gaba da wannan aiki don kuwa... muna ƙoƙarin ganin ƙannenmu su ci gaba da karatu."
"Ba zai yiwu saboda abu ya faru a ce ƙannenmu su daina karatu ba," in ji Hauwa.
Makaranta guda ɗaya ce kacal ta rage a garin Chibok kuma duk yaran yankin a nan suke gwamutsuwa
An tambayi shugaban ƙaramar hukumar Chibok, Yagar Yakawa ko me ya dakatar da aikin gina sakandaren, sai ya ce su ma ba su sani ba.
"Da aka biya su wajen naira miliyan 750, suka yi azuzuwa. Suka giggina sauran ba mu san meye ne ya faru ba. In an yi magana sai su ce za su zo, za su zo."
Ya ce "Sashen ayyukan injiniyan sojan ƙasar aka ba kwangilar. Kuma har yanzu ba su zo (sun kammala) ba."
Sake gina sakandaren 'yan mata ta Chibok ga alama ba kawai zai bai wa ƙannensu Hauwa damar zuwa makaranta ba ne, zai ma rage musu baƙin taɓon da ya firgita rayuwarsu da ma duniya baki ɗaya.