'Ba a damuwa kan sauran mutanen da Boko Haram ke sacewa'

Army
Bayanan hoto,

Amnesty International ta ce duk da nasarorin sojan Nijeriya a fagen daga amma ba a nuna damuwa kan mutanen da ake ci gaba da sacewa

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta ce an sace ɗumbin mutane lokaci guda fiye da sau arba'in tun a cikin shekara uku bayan 'yan matan sakandaren Chibok.

Amnesty ta ce yayin da gwamnati ke ƙoƙarin gaske don kuɓutar da 'yan matan Chibok, sauran waɗanda ake sacewa ba sa samun kulawa irin wannan.

A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne, mayaƙan Boko Haram suka auka kan makarantar sakandaren 'yan mata ta Chibok kuma suka awon gaba da wasu kimanin 300.

Ya zuwa sama da 20 ne a cikin 'yan mata aka iya kuɓutar da su, yayin da fiye da 200 ke hannun Boko Haram.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari

Rundunar sojin Nijeriya ta yi nasarar fatattakar 'yan tada-ƙayar-bayan daga dajin Sambisa amma har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare.

Haka kuma, dakarun sojin ƙasar lokaci zuwa lokaci sukan bayyana ƙwato ɗaruruwan mutane akasari mata da ƙananan yara a hannun ƙungiyar.

Wakilin BBC Martin Patience ya ce "Duk da nasarar da sojoji suke samu a yaƙin da suke yi, har yanzu ana sace mutane. Kuma a cewar Amnesty ba a nuna damuwa kan waɗannan sace-sace."

Don haka ta buƙaci gwamnati ta ƙara zage dantse wajen dakatar da 'yan tada-ƙayar-bayan Boko Haram far wa mutane kusan a kullu yaumin.

A cewar Amnesty mayaƙan Boko Haram kan yi amfani da tarzomar da ta yi daidai da aikata laifukan yaƙi wajen far wa fararen hula.