Tsohon shugaban PDP ya musanta mallakar N13bn da aka gano

Aljahi Adamu Mu'azu a wani taron PDP

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watan Mayun 2015 ne Alhaji Adamu Mu'azu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban PDP

Tsohon shugaban babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP, Alhaji Ahmadu Adamu Mua'azu ya ce kudin da hukumar yaki da yiwa arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta gano a wani gida ba nasa ba ne.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook, inda ya ce hakika shi ya gina gidajen, amma tuni ya sayar da su ba tare da sanin ko waye ya saye su ba.

"Na fara harkar gidaje tun a shekarar 1983 kuma na gina tare da sayar da gidaje da dama a fadin duniya. Gidan da ake magana akai na daya daga cikinsu. Na samu filin kuma mun yi hadin guiwa wajen gida gidajen ta hanayr bashin da na samu a banki shekaru tara da suka wuce."

Inda ya kara da cewa an sayar da duka gidajen ga mutane domin biyan bashin

"A don haka ba ni da masaniyar wadanada suka sayi gidajen ko kuma skue haya a cikinsu."

Alhaji Adamu Mu'azu ya kuma bayyana cewa ya yi amannar cewa gaskiya za ta yi halinta a binciken da EFCC ke yi domin gano wanda ya mallaki kudin.

Wata babbar kotun tarayyar da ke Lagos ta mika wa gwamnatin kasar makudan kudin na wucin gadi a ranar Alhamis.

A ranar Larabar da ta wuce ne EFCC ta gano zunzurutun kudin $43,449,947, £27,800 da kuma N23,218,000 a wani tafkeken gida da ke unguwar Ikoyi, a birnin na Lagos.

EFCC dai ta ce ta gano kudin ne da yawansu ya kai naira biliyan 13, yayin da ta kai samame a gidan, wanda babu kowa a cikinsa.

Samamen ya biyo bayan bayanan sirri da ofishin hukumar reshen jihar Lagos ya samu ne daga masu fallasa barayi, inda suka shaida wa EFCC cewa suna zargin irin shige da ficen da ake yi da manyan jakunkuna a gidan.