Arsenal na fuskantar babban kalubale - Wenger

Arsene Wenger

Asalin hoton, AFP

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce suna fuskantar "babban kalubale" wajen cancantar shiga gasar cin kofin Zakarun Turai, yana mai cewa babu abin dsa ya sauyawa game da makomarsa a kungiyar.

Kashin da Crystal Palace ta bai wa Arsenal da ci 3-0 ranar Litinin ya mayar da kungiyar a matsayi na shida, inda take bayan Manchester City, wacce ke matsayi na hudu, da maki hudu koda yake tana da ragowar wasanni takwas.

Wenger, wanda kwantaraginsa zai kare a lokacin bazarar da ke tafe, ya jagoranci Arsenal zuwa matsayi na hudun farko a teburin gasar a dukkan kakar wasa 20 da suka buga.

Da aka tambaye shi game da yiwuwar shirin cikin 'yan hudun farko, sai ya ce: "Watakila za mu iya kai wa wannan matsayi, mai yiwuwa kuma ba za mu kai ba."

An amince a bai wa Wenger karin wa'adin shekara biyu a kungiyar, koda yake har yanzu bai yanke shawara kan ko zai ci gaba da horas da 'yan wasan ba.

Dokewar da aka yi wa Arsenal sau biyar a cikin wasanni goma da ta fafata a gasar Premier ta sanya wasu magoya bayan kungiya na yin kira ga Wenger ya ajiye mukaminsa.

Da aka tambaye shi ranar Juma'a game da makomarsa, Wenger ya ce: "Ban san abin da magabatan kungiyar ke tattaunawa game da ni ba. Ni dai kawai ina yin aikina, inda na mayar da hankali kan yadda za mu ci wasa da kuma yadda masu goyon bayanmu za su ga irin rawar da muke takawa."

Arsenal za ta bakunci Middlesbrough ranar Litinin.

Wenger ya ki yin tsokaci kan rahotannin da ke cewa za a rika biyan sabon albashin dan wasan gaba Alexis Sanchez £300,000 a kowanne mako.