Ba yanzu zan sanar da makomata a Arsenal ba - Ozil

Mesut Ozil

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Arsenal ta sayi Mesut Ozil a kan £42m daga Real Madrid a 2013

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya ce zai bari sai lokacin bazara kafin ya sanar da makomarsa a kungiyar.

Ozil, dan shekara 28, na da sauran shekara daya kafin kwantaraginsa ta kare a kungiyar bayan ya koma Arsenal daga Real Madrid a 2013.

Sai dai dan kasar ta Jamus yana son taimakwa Arsenal domin ta gama kakar wasa ta bana a cikin 'yan hudun farko da ke saman teburin gasar Premier sanna ta samu gurbi a gasar cin kofin Zakarun Turai kafin ya sanar da makomarsa.

Ozil ya shaida wa Sky Sports cewa "A halin da ake ciki abin da ya fi muhimmanci shi ne Arsenal, ba ni ko wani dan wasa ba". Kungiyar tana fuskantar kalubale da dama, kuma a wannan matsayi ba ni ne nake da muhimmanci ba - kungiyar ce ke da muhimmanci."

A cewarsa, "Za mu tattauna a lokacin bazara domin fayyace komai. A halin yanzu bai kamata a yi magana kan makomata ba."

Kocin kungiyar Arsene Wenger yana fuskantar sabuwar suka daga wajen magoya baya tun da suka sha kashi a hannun Crystal Palace da ci 3-0 ranar litinin, sai dai Ozil ya ce Wenger "ya cancanci a girmama shi" saboda rawar da ya taka.