An kashe 'yan sandan Tanzania a wani kwanton ɓauna

map

Wasu 'yan bindiga sun kashe 'yan sandan Tanzania akalla takwas a wani harin kwanton bauna da suka kai mus a kan hanya ranar Alhamis da daddare, in ji wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce an kai wa 'yan sandan hari ne a lokacin da suke dawowa daga sintiri a kauyen Bungu mai nisan kilomita 110 daga yammacin Dar es Salaam, babban birnin kasar.

'Yan sanda sun ce sun mayar da raddi kan 'yan bindigar har zuwa maboyarsu inda suka kashe hudu daga cikinsu a harbe-harben da bangarorin biyu suka yi.

Shugaban kasar John Magufuli hya nuna matukar takacinsa a kan kisan da aka yi wa jami'an tsaron.

'Yan sanda sun ce 'yan bindiga ne suka kai mus harin, kuma sun sace makamansu.

Wakilin BBC a Tanzani Sammy Awami ya ce ana yawan kai hari kan 'yan sanda da ofisoshinsu sannan a kwace makamansu a kasar.

Rahotanni sun ambato ministan cikin gida Mwigulu Nchemba na cewa an kaddamar da gagarumin bincike kan wadannan hare-hare.