Messi ya sake sharewa Barca hawaye

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An zura dukkan kwallayen ne kafin a tafi hutun rabin lokaci

Lionel Messi ya zura kwallo biyu a wasan da Barcelona ta doke Real Sociedad 3-2, lamarin da ya sanya mata fatan komawa kan dawonta a gasar La Liga.

Barca na bayan Real Madrid da maki uku, kuma Madrid za ta buga El Clasico a karshen makon gobe.

Messi yazura kwallon farko ne daga nisan yadi 25, kuma ya soka kwallo ta biyu, wacce ta zama 498 da ya ci wa kungiyar, kafin Samuel Umtiti ya ci kwallon da ta bai wa La Real kwarin gwiwa.

Paco Alcacer ne ya zura kwallo ta uku inda suka kasance da ci 3-1 kafin Xabi Prieto ya sake ci wa Sociedad tasu kwallon.

Barcelona za ta karbi bakuncin Juventus ranar Laraba a wasan kwata-fainal na gasar cin kofin zakarun turai, bayan ta sha kashi a zagayen farko na wasan da ci 3-0 a Italiya.