Manchester City ta kusa kai wa gaci

Vincent Kompany

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kompany ya zura kwallonsa ta farko a cikin wata 20

Manchester City ta karfafa matsayinta na kasance a sawun 'yan hudu na gasar Premier bayan ta doke Southampton da ci 3-0.

Dan wasan da ya sha fama da jinya Vincent Kompany ya sanya kansa ya doka kwallon da David Silva ya bugo masa wacce ta zama kwallon farko da ci a cikin watan 20.

Leroy Sane da Sergio Aguero suka zura kwallo ta biyu da ta uku.

Yanzu dai City ce ke matsayi na uku a saman teburin gasar ta Premier, inda suka yi wa Everton mai matsayi na biyar tazarar maki bakwai.

Magoya bayan City da dama na ganin da ana sanya Company a wasa da kungiyar ta kai kusa da Chelsea.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Magoya bayan City da dama na ganin da ana sanya Company a wasa da kungiyar ta kai kusa da Chelsea.