Turkey: Erdogan zai iya mulki har 2029

Shugaba Erdogan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba, gwamnatin Turkiyya ke daukar matakin kame duk wanda ake zargi da aikata ta'addanci

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya sha da kyar a zaben raba gardama da aka yi a kasar ranar Lahadi kan fadada tsawon lokacin da shugaban kasa zai yi yana mulki.

Yanzu haka dai shugaba Erdogan zai iya tsayawa takara har sau biyu da za ta ba shi damar kasancewa a ofis har zuwa 2029.

Daga cikin kaso 99.45 na kuri'un da aka kidaya, an samu kaso 51.37 da suka zabi amincewa da tsawaita mulkin, a inda kuma wadanda ba sa so suka kasance kaso 48.63.

Hakan ne kuma ya sa hukumar da ta gudanar da zaben ta ba wa wadanda suka zabi amincewa da tazarce nasara.

Asalin hoton, EPA

Magoya bayan shugaba Erdogan sun ce maye gurbin tsarin mulki na firaiminista da na shugaba mai cikakken iko zai zamanantar da siyasar kasar.

Sai dai kuma manyan jam'iyyun adawa na kasar sun ce ba su amince da sakamakon ba kuma za su kalubalanci shi.

Jam'iyyar Republican People's Party (CHP) dai ta nemi da a sake kidayar kaso 60 da kuri'un da aka kada.

Har wa yau jam'iyyar ta soki hukuncin da hukumar zaben ta yanke na amince wa da kuri'un da ba bu sitamfi a kansu.

A dai-dai lokacin da magoya bayan Erdoan suke zaga gari suna murna, su kuwa masu hamayya sun ta kwala tukwane da kasa a birnin Istanbul, a wata hanyar nuna bacin rai a gargajiyance.

Rahotanni sun ce an harbi masu zanga-zanga mutum uku a kusa da wani ofishin 'yan sanda da ke kudu maso gabashin lardin Diyarbakir, a rumfar zabe.

Shugaba Erdogan dai ya zama shugaban kasar ta Turkiyya a 2014, bayan kwashe fiye da shekara 10 yana firai minista.

Kundin zabe ya nuna cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa ranar 3 ga Nuwamban 2019.

Shugaban kasa zai yi wa'adin shekara biyar har karo biyu.

Asalin hoton, AFP