'Barayin kudaden gwamnati na boye kudi a Makabarta'

Ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Minista Lai ya ce kishin kasa ne yasa wasu 'yan Najeriya ke tona asirin barayin gwamnati

Ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Lai Muhammed, ya yaba wa 'yan Najeriya game da yadda suke taimaka wa gwamnati a yakin da take da cin hanci da rashawa.

A wata sanarwar da ta fito daga ofishinsa, ministan ya ce mutane na bayar da bayanai kan yadda 'barayin' da suka saci kudaden gwamnati ke boye kudaden a wuraren da suka hada da Makabarta.

"Ana shaida mana yadda ta kai har barayin gwamnati na boye kudade a rami a cikin gidajensu da kuma cikin surkukin daji har ma da Makabartu."

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta gano makudan kudade ciki har da miliyoyin daloli da fama-famai da kuma dubban miliyoyin naira.

Ministan ya kuma yaba wa tsarin kwarmata bayanan da gwamnati ta bullo da shi, wanda ya ce ya taimaka gaya wajen gano kudaden da aka sace da dama.

Alhaji Lai ya kuma ce gwamnati za ta bayyana wa 'yan Najeriya adadin kudaden da gwamnati ta kwato bayan an kammala shari'un da ke gaban kotu da suka shafe su.

Inda ya kara jaddada cewa kudaden suna nan a ajiye babu abin da ya same su, kana ya kara mika bukatar mutane su ci gaba da samar da bayanai ga gwamnatin.