Falasdinawa da ke kurkuku a Isra'ila na yajin cin abinci

Falasdinawa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mista Barghouti na daya daga ckin wadanda aka tsare a kurkuku a Isra'ila

Falasdinawa fiye da 1000 da ke gidan yari a Isra'ila na yajin cin abinci domin nuna rashin amincewa da yanayin da suke ciki.

Shugaban Falasdinawa, Marwan Barghouti da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai domin kashe mutane biyar ne ke jagorantar matakin yajin cin abincin.

Mista Barghouti mai goyon bayan gwamnatin shugaba Mahmoud Abbas' Fatah ne, kuma ana ganin mai yuwa shi zai gaji Mista Abbas.

Ana kuma fargabar cewa yajin cin abincin wanda Falasdinawa 1,187 ke yi zai iya janyo zaman dar-dar a yankunan falasdinawa.

Yajin cin abincin ya zo daidai kewayowar ranar da Falasdinawa suka kebe domin tunawa da 'yan uwansu dake tsare a gidan yarin Isra'ila, wanda suke yi duk shekara.

Falasdinawa na daukar mutanen da aka tsare a matsayin fursunonin siyasa, inda yawancinsu aka samesu da aikata laifukan da suka hada da kai hare-hare a kan Isra'ila.

Yayin wasu kuma ake tsare da su karkashin wata doka wadda ta bai wa hukumar Isra'ila damar tsare mutane har tsawon watanni shida ba tare da an tuhume su ba.

Kungiyoyin kula da fursunoni a kasar sun bayyana cewa a shekarar da ta gabata Falasdinawa fursunoni 7000 ne a gidan yarin Isra'ila.