Jirgin Ethiopia ya sauka a filin jiragen sama na Abuja

Jirgin Ethiopia

Asalin hoton, FAAN

Bayanan hoto,

An dai kashe kusan naira biliyan shida wajen gyaran filin jirgin na Abuja

Gwamnatin Najeriya ta bude filin jirgin sama na Abuja domin ci gaba da sufurin jirage.

Inda jirgin saman Ethiopia ya zama jirgi na farko da ya fara sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a ranar Talata.

An fara zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin ne kwana daya kafin cikar wa'adin makonni shida da gwamnati ta diba na rufe filin saboda gyaran titin sauka da tashin jirage.

Ko da yake an kammala ginin sabon titin jirgin mai tsawon kilomita 3.6, akwai rahotanni da ke cewa za a ci gaba da sauran gyare-gyaren da suka rage a filin jirgin da daddare.

Wani babban jami'i a ma'aikatar sufurin jiragen sama ta Najeriya, Ibrahim Idris ya shaida wa BBC cewa "Kamfanin jiragen sama na Ethiopia ya amince ya fara tashi daga filin jirgin saman a ranar Talata."

An rufe filin jirgin saman na Abuja ne a ranar takwas ga watan Maris domin yin manyan gyare-gyare, ciki har da sake gina titunan sauka da tashin jirage.

Kafin bude filin jirgin sai da shugaban hukumar sa ido kan sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) Usman Muktar, ya je filin jirgin a ranar Litinin inda ya tabbatar da ingancin gyare-gyaren da aka yi kafin ya nuna amincewarsa a bude filin.

An karkatar da jiragen saman da ke zirga-zirga a filin jiragen na Abuja zuwa filin jiragen sama na Kaduna a tsawon makonnin da aka yi ana gyaran.

Sai dai wasu manya-manyan kamfanonin jiragen saman na kasashen waje kamar Lufthansa da kuma British Airways basu dinga amfani da filin jirgin na Kaduna ba a lokacin da aka rufe na Abuja.

Sai dai mutanen da rayuwarsu ta dogara da filin jirgin na Abuja, kamar masu kananan sana'oi sun nuna farin ciki sake bude filin jirgin.