Isra'ila: Ba za mu yi sulhu da Falasdinawa masu yajin cin abinci ba

Falasdinawa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Falasdinawa sun ce wadanda ake tsare da su fursunonin siyasa ne, yayin da Isra'ila ta bayyana su da " 'yan ta'adda"

Hukumomin Isra'ila sun ce ba za su nemi yin sulhu da Falasdinawa fiye da 1000 wadanda suka fara yajin cin abinci don nuna rashin amince da yanayin da suke ciki a gidajen yarin Isra'ila ba.

Wani jagoran Falasdinawa, Marwan Barghouti da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai sabo da kashe mutane biyar ne, yake jagorantar matakin yajin cin abincin.

Mista Barghouti mai goyon bayan gwamnatin shugaba Mahmoud Abbas ne, kuma ana ganin mai yuwa shi zai gaji Mista Abbas.

Hukumomin Isra'ila sun tsare shi a wani dakin gidan yari shi kadai saboda kiran yajin cin abincin da ya yi, wanda a ranar Talata ya shiga rana ta biyu.

Har ila yau, sun ce "Barghouti yana jawo bore kuma jagorantar yajin cin abinci ya sabawa dokokin gidan yarin."

Hakazalika, wani ministan Isra'ila Gilad Erdan ya ce "babu dalilin da zai sa mu nemi sulhu. 'Yan ta'adda ne, masu kisan mutane wadanda ke tsare suke samun abin da ya dace da su".

An kama wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna goyon baya ga fursunonin da ke tsare a yankin da aka mamaye a Gabar Yammacin kogin Jordan a ranar Litinin, ranar farko ta yajin cin abinci. Wasu kuma matasa sun yi ta arangama da jami'an tsaron Isra'ila a birnin Bethlehem.

Ana kuma fargabar cewa yajin cin abincin wanda Falasdinawa 1,187 ke yi zai iya janyo zaman dar-dar a yankunan falasdinawa.

Batun tsare Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila wani abu ne da yake kawo zaman tankiya tsakanin bangarorin biyu.

Falasdinawa suna yi wa wadanda aka tsare kallon fursunonin siyasa.

Kungiyoyin kula da fursunoni a kasar sun bayyana cewa a shekarar da ta gabata Falasdinawa fursunoni 7000 ne a gidan yarin Isra'ila.