'Buhun masara ne ya cece ni a Malawi'

Wani mutum a kwale kwale

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tafkin Malawi na daya daga cikin manyan Tafkuna a Afirka

Wani dattijo mai shekaru 67 ya ce ya tsira da ran shi ne a lokacin da ya makale a jikin wani buhun garin masara bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tafkin Malawi.

Graciam Kodowe na daya daga cikin fasinjoji 54 da suka tsira da ransu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a lokacin da ake wata iska mai karfin gaske a ranar Lahadi.

'Yan sanda sun ce mutum biyar sun nutse yayin da kuma ba a ga wasu mutum 11 ba.

Kwale-kwalen na cike makil da mutanen da ke dawowa daga hutun Easter ne, a lokacin da ya kife a kauyen Rumphi da ke wani yanki a arewacin Malawi.

Mista Kondowe ya shaida wa gidan radion Zodiac da ke kasar cewa wata iska mai karfi ce ta rinjayi kwale-kwalen mintuna 15 da fara tafiyarsu a tafkin.

Ya kara da cewa ma'aikatan jirgin sun yanke shawarar su koma inda suka taso, amma kuma sai kwale-kwalen ya kife kafin su isa.

Mista Kondowe ya ce ya makale a jikin wani buhun garin masara da ya fado daga cikin kwale-kwalen sannan daga nan ya yi ninkaya zuwa bakin tafkin inda ya tsira da ransa.

Wani dan sanda, Denis Banda ya ce mutum takwas da suka rayu daga cikin 54 na asibiti inda suke samun kulawa bayan sun ji rauni.

Wani dan jarida a Malawi, Joab Chakhaza ya shaida wa BBC cewa, mazauna yankin sun yi amfani da kwale-kwale wajen ceto akasarin fasinjojin.

Ya kara da cewa ana kan neman mutum 11 da har yanzu ba a san inda suke ba, amma kuma zai yi wuya a same su da ransu.

An saba amfani da kwale-kwale a matsayin hanyar da ake sufuri a tafkin Malawin kuma ba a cika samun aukuwar irin wannan lamari ba.

A shekarar 2012, 'yan cirani 47 da ke tserewa daga rikici da ya faru a Somaliya da Habasha suka nutse a tafkin bayan jirginsu ya kife.