Yara 68 sun mutu a wani harin Syria

Bas din da aka sakawa bam

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Bas din ya dauko 'yan gudun hijirar Syria da aka dauko daga garuruwan da ke karkashin ikon gwamnati

Wata mota dake cike makil da abubuwan fashewa ta afka cikin jerin gwanon motoci a kusa da Aleppo.

Kungiyar kare hakkin bil adama dake sa ido kan Syria dake Burtaniya ta ce an kashe akalla mutum 109 dake barin garuruwan dake karkashin ikon gwamnati tare da masu aikin agaji da sojojin 'yan tawaye.

Kungiyar ta kara da cewa wasu da dama kuma sun jikkata a harin.

Fashewar ta yi kaca-kaca da bas bas din, kuma wasu motocin sun kama da wuta, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, haka kuma fashewar ta bar gawarwaki da dama a kasa, a daidai lokacin da jerin gwanon motocin suke jira a kusa da yankin 'yan tawaye da ke Aleppo.

Rahotanni na cewa a bangare guda kuma, mutane da dama , wadanda akasarinsu yara ne sun jikkata sakamakon bam da aka saka a Damashka, babban birnin kasar.

Kafafen yada labaran kasar sun rawaito cewar akalla bamabamai uku aka saka kusa da dandalin tsakiyar dandalin Umayya.

Hari mai muni

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wasu yara da suka jikkata na samun kulawa a garin Aleppo dake karkashin ikon gwamnati

An fitar da akasarin mutanen da aka kai wa hari ranar asabar ne daga Foah da Kefraya, garuruwan 'yan shia dake karkashin ikon gwamnati wanda ke kewaye da 'yan tawaye da 'yan kungiyar al-Qaeda tun shekarar 2015.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin harin da aka kai kan bas din.

A jawabin da ya gabatar ranar Lahadi ta gabata, Pope Francis ya kira harin da " Hari mai muni" kan 'yan gudun hijira dake tserewa.

Ya kara da cewa " Allah ya kare wadanda ke kokarin samar da kwanciyar hankali da fararen hula da Syria, wadanda ke matukar shan wahala sakamakon yaki da yaki kawo karshen tashin hankali da kisa".