Ethiopia ta yi watsi da binciken MDD

wasu masu zanga zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga zanga daga yankunan Amhara da Oromio na korafi kan wariya a fannin tattalin arziki da siyasa.

A karon farko, Firai ministan Habasha ya yi watsi da kiran da majalisar dinkin duniya da tarayyar Turai ke yi na gudanar da bincike kan daruruwan mutane da suka mutu a watannin da aka shafe ana zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Hailemariam Desalegn ya ce kasar zata iya yin binciken da kanta.

Masu zanga-zanga daga yankunan Amhara da Oromio na korafi kan wariya a fannin tattalin arziki da siyasa.

Gwamnati ta saka dokar ta baci a wani martani kan zanga zangar.

Kasar ta fuskanci zanga-zangar da bata taba ganin irinta ba, wacce aka yi ta baya bayan nan a watan Nuwambar shekarar 2015.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun ce daruruwan mutane sun rasa rayukansu a lamarin inda 'yan sanda da masu zanga zangar suka yi gwabza.

A baya dai gwamnatin ta musanta adadin mutanen, kuma ta ce jami'an tsaro na duba yadda za su shawo kan abinda aka kira "sojojin kin zaman lafiya".

Mista Hailemariam ya shaidawa wakilin BBC, Emmanuel Igunza cewa hanyar da kawai za a bi domin shawo kan matsalar ita ce hukumar kare hakkin bil'adama da kasar ta samar karkashin kudin tsarin mulki ta duba hanyar da za ta bi domin ta shawo kan lamarin.

Bayanan hoto,

Gwamnati ta saka dokar ta baci a wani martani kan zanga zangar

Ya ce hukuma ce mai zaman kanta amma kuma ya amince cewar "baza ta iya ba" ya kuma kara da cewa za a iya karfafa hukumar.

Ya kara da cewa ya kamata a girmama 'yancin Habasha kuma ya yi watsi da binciken da za a yi a wajen kasar.

A watan Agustan bara ne Kwamishinan majalisar dinkin duniya dake kare hakki bil'adama ya yi kira ga masu sa ido na kasa da kasa su yi bincike kan kashe-kashen, bayan sun yi zargin jami'an tsaro sun yi amfani da harsasai kan masu zanga zanga a yankunan Amhara da Oromia.

Kiran da tarayyar turai ta nanata a watan Oktoba ta kuma kara nanatawa a makon da ya gabata.