Theresa May ta bukaci a gudanar da zaben ba zata a watan Yuni

Theresa May
Bayanan hoto,

Theresa May na jawabi akan gudanar da zabe nan ba da dadewa ba

Farayi Ministar Birtaniya,Theresa May ta ba da sanarwar shirye-shiryen gudanar da zaben ba zata a rana 8 ga watan Yuni.

Misis May ta ce Britaniya na bukatar yanayi na tabbas da zaman lafiya da shugabanci mai dorewa bayan zaben raba gardamar ficewa daga Tarayyar Turai.

Da Misis May ke bayani kan shawarar da aka dauka, ta ce '' kan jama'ar kasar a hade yake, amma 'yan majalisa kansu a rabe yake.''

A ranar Laraba ne, za a kada kuri'a a majalisar wakilai kan shawarar gudanar da zaben.

Firayi ministar na bukatar amincewar majalisa gabanin gudana da zaben kafin lokacin da aka tsara yinsa a 2020.

A lokacin da Misis May ke bayyana dalilan da ya sa ta yanke shawarar gudanar da zabe yanzu, ta ce'' Na tabbatar da cewa ta gudanar da wannan zabe zamu samu yakini da ingantancin tsaro a nan gaba.

Misis May ta zargi sauran jam'iyyun siyasa da yin ''bita da kulli'' inda ta kara da cewa ''yin hakan zai zama hadari ga nasarar ficewa daga kunigiyar Tarayyar Turai da rashin tabbas da kuma rashin zaman lafiya a kasar. Don haka muna bukatar a gudanar da zabe kuma muna bukatar yin hakan yanzu.''

Ta kara da cewa '' Bamu da wata dama da ta wuce wannan, na gudanar da zaben yayin da kungiyar Tarayyar Turai ke shawarwari akan matsayin da za ta dauka kafin a fara cikakkiyar tattaunawa akan lamarin.''

''Nan bada dadewaba na yanke wannan shawara. Tun lokacin da na zama Firayim Minista, na ce ba za a a gudanar da zabe ba sai shekara ta 2020, amma yanzu na amince cewa hanyar da zamu iya tabbatar da yakini da tsaro a nan gaba, ita ce a gudanar da zabe kuma ina bukatar goyon bayan ku akan shawarar da dole ne mu dauka.'' Inji Theresa May

A wata sanarwa a wajen fadar Firayi minista, Misis May ta ce jam'iyyar Labour ta yi barazanar kin amincewa da yarjejeniyar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, jam'iyyar Liberal Democrats kuma ta riga ta ce tana da niyyar ganin al'amurran gwamnati sun tsaya cak, ita kuma jam'iyyar Scottish National ta sha alwashin kada kuri'a domin nuna rashin amincewa kan ficewar Britaniya daga kungiyar Tarayyar Turai.

Haka suma yan Majalisar dattawa sun sha alwashin cewa''zasu kalubalancemu ta kowace hanya kan wannan mataki da muka dauka.'' Inji firayi ministar

Misis May ta kara da cewa ''Idan ba mu gudanar da zabe yanzu ba, bita da kullin siyasa da ke gudana zai ci gaba, kuma tattaunawar da muke yi da kungiyar Tarayyar Turai za ta yi wuya a nan gaba.''

Shugaban jam'iyyar Labour Mista Corbyn ya ce ya amince da shawarar da firayi minista da dauka, inda ta kara da cewa '' yin hakan zai ba 'yan Britaniya damar zaban gwamnatin da za ta kare hakkin masu rinjaye, da ya hada da kula da harkokin gine-gine da ilimi da kiwon lafiya da kuma tattalin arzikin kasar.''

A lokacin da Shugaban Liberal Democrats Tim Farron ke mayar da martani akan jawabin Misis May ya rubuta akan shafinsa na tweeter cewa '' Wannan dama ce ta sake hanyar da kasar za ta bi a nan gaba.