'Bai kamata a gina kasuwa a masallacin idin Kano ba'

Masallacin Idi na Kano
Bayanan hoto,

Wasu malamai sun ce bai kamata gwamnatin jihar Kano da rage filin masallacin Idi don gina kasuwa ba

Wasu malaman addinin musulunci a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta ba da damar gina shaguna a babban masallacin idi na birni.

Malaman sun nuna damuwa ne kan barazanar da suka ce masallacin Idin na Kano mai tsohon tarihi ke fukanta, ta hanyar mayar da shi wajen kasuwanci.

A cewar malaman hakan bai dace ba, don kuwa babban kuskure ne zaftare wannan wajen ibada mai tsohon tarihi maimakon bunƙasa shi.

Masallacin idin wanda ya yi iyaka da ƙofar mata da Fagge, yana kuma fuskantar barazana daga manyan kasuwannin Kantin kwari da Ƙofar wambai waɗanda suka sanya shi a tsakiya.

Sheikh Abba Adamu ya ce ''Kasuwa ko ina take muna murna da ita, amma filin Idi a rage shi don gina shaguna bai dace ba, babban kuskure ne.''

A yanzu haka, ana amfani da makeken filin wajen ajiye motoci da kuma a matsayin tasha, inda gwamnati ke karɓar haraji daga masu motocin haya da ke ɗaukar kayan 'yan kasuwa.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a nasa ɓangare cewa ya yi masallacin idi na birnin Kano ya shafe sama da shekara 200 don haka bai kamata gwamnati ta yi wani tunani na rage shi ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce '' Wannan fili ne mai tarihi, kuma babbar alama ce ta addinin musulunci a jihar Kano, rage shi bai dace ba ko kadan''

An dasa harsashin gini

Wakilin BBC da ya kai ziyara filin Idin ya ce ya ga wurin da aka fara aza harsashin gini a masallacin, abin da ke nuna alamar ana fitar da ginin kasuwa.

Ya ce filin ya zama tashar mota, inda direbobi ke yin lodin fasinjoji zuwa garuruwa a ciki.

Gwamnatin Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ce dai ta fara mayar da filin zuwa wajen ajiye motoci da ɗaukar kaya da fasinjoji.

A cewarta matakin zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da ake samu a kewayen manyan kasuwannin yankin.

Sheikh Tijjani Usman ya ce bai kamata idan ba a inganta filin Idi ba, a kuma ce za a rage shi ba.

Ya kuma ce '' Kamata ya yi ma wannan fili a kara bunkasa shi, in ma da dama a saka lemomi, wadanda in ana ruwa ko kuma rana sai a rika bude su don mutane su rika ibada cikin kwanciyar hankali.''

Sai dai kuma a wata takarda da BBC ta samu dauke da kunshin bayanin sakamakon zaman taron majalisar zartarwar jihar Kano, ta nuna cewa gwamnati ta ba da umarnin soke damar gina shagunan.