Sojojin Saudia 12 sun mutu a Yemen

Sojojin kasar Saudiyya 12 ne suka mutu a wani hadarin jirgin saman soji a kasar Yeman, kamar yadda dakarun kawancen hadin gwiwa da ke yaki da 'yan tawayen Yemen suka bayyana.

Jirgin ya yi hadari ne a lardin Marib da ke gabashin babban birnin kasar Sana'a.

Asalin hoton, AFP/GETTY

Bayanan hoto,

Dakarun da suke mara wa shugaban Yemen baya sun kwashe shekara biyu suna yaki da 'yan tawayen Houthi

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ce ba a san dalilin da ya janyo hadarin ba tukuna, sai dai ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan hakan.

Kawancen hadin gwiwa da Saudiya ke wa jagoranci yana goyon bayan gwamnatin kasar ne a yakin da take da 'yan tawayen Houthi da kawayensu.

A watan jiya ne 'yan tawayen suka ce sun yi nasarar kakkabo wani jirgi mai saukar ungulu mallakin Saudiyya a tashar jiragen ruwa ta Maliya a garin Hudaydah, wanda yake karkashin ikon 'yan tawayen.

Dakarun da suke mara wa shugaban kasar Yemen Abdrabbuh Mansour Hadi baya, sun kwashe shekara biyu suna yaki da 'yan tawayen Houthin.

Fiye da mutum 7,600 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu dubu 42 suka jikkata tun bayan fara yakin, galibinsu a hare-hare ta sama da kawancen da Saudiyya take jagoranta wanda yake mara wa Shugaba Hadi baya, wanda aka kore shi daga Sana'a a watan Fabrairun shekarar 2015.

Rikicin da kuma toshe hanyoyin isa kasar da kawancen ya yi, ya haddasa yanayi na rashin abinci da ruwa da kuma muhalli, inda fiye da kaso 70 cikin 100 na mutanen kasar suka tsinki kansu a ciki.