Yaƙi da cin hancin Nigeria duk hira ce - Sule Lamiɗo

Sule Lamido
Image caption Hukumar EFCC ta gurfanar da Sule Lamiɗo da 'ya'yansa biyu a gaban kotu, bisa zargin almundahana da kudaden al'umma a lokacin da yake mulkin jihar Jigawa.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya bayyana tababa a kan yaƙin da gwamnatin Muhammadu Buhari ke cewa tana yi da cin hanci da rashawa.

A cewarsa batun duk hira ce, don kuwa shi ma jagoran gwamnatin yana da tabon rashawa lokacin da ya yi aiki a gwamnatin Janar Sani Abacha.

"A wancan lokacin dai ya yi aiki da Abacha. Kuma shi ne na kusa-kusa da shi. In rashawa ce, me ake faɗa kansa a sannan?"

Ya ce "abubuwan da ake faɗa kan batun tsaro da rashawa, ina ganin gaskiyar maganar ita ce (Shugaba Muhammadu Buhari) yana yi ne a kan matsayin hira. Ba don gaskiya ba."

Ƙusoshin jam'iyyar adawa ta PDP irinsu Lamiɗo na ganin yaƙi da cin hancin da gwamnatin APC ke yi, ya fi karkata a kan jami'an gwamnatin PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki a Nijeriya.

Sule Lamiɗo wanda yake a matsayin beli kan tuhumar cin hanci da hukumar EFCC ke yi masa a gaban kotu, ya ce akwai rainin hankali kan yadda ake cewa an bankaɗo maƙudan kuɗi amma ba a san mai su ba.

"Akwai rainin hankali a cewa hukumar EFCC ta je wani gida a Legas ta binciko kuɗi. Shin wa ya ba ta labarin wannan gidan? Ai akwai shi! Kuma mai ba da labarin wa ya ce ya mallaki kuɗin?"

Ya ce zancen kawai ne a ce hukumar leƙen asiri ta ƙasa NIA ta rasa inda za ta ajiye kuɗinta sai ta kai su wani gida can a Legas.

Tsohon ministan harkokin wajen Nijeriyar, ya buƙaci shugabanni su riƙa faɗa wa mabiyansu gaskiya, maimakon biye wa son rai a kan rashin gaskiya ba.

"Muddin za ka nemi muƙami a Nijeriya, ka neme shi a kan matsayin hankali, a kan hujjar (gina) ƙasa da yanayin shugabanci a duniya."

Kada yanayin haukan ƙasa ya firgata ka, ka biye masa, in ji Lamiɗo.

A cewarsa kamata yi a ce "muna da ƙarfin zuciya da ƙarfin imanin da ke sa wa, mu tsaya a kan gaskiya, ko da 'ya'yanmu za su ce ba su yarda ba."

Labarai masu alaka