'Ba mu halarci bikin auren 'yan luwadi a Zaria ba'

Gay Nigerian
Image caption An haramta luwadi da madugo a Najeriya

Jami'an tsaro a Najeriya sun gurfanar da wasu mutum 53 a gaban kotu da zargin shirya wa da kuma halartar bikin auren jinsi a wani otel a garin Zariya.

Mutanen, wadanda aka kama ranar 15 ga watan Afrilu, sun musanta zargin da ake yi musu na hada baki, da yin taro ba bisa ka'ida ba, da kasancewa mambobin haramtacciyar kungiya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya rawaito cewa mutanen sun gurfana ne a gaban kotun majistiri da ke unguwar Chediya a garin na Zariya.

Mai gabatar da kara Mannir Nasir ya ce laifukan sun saba wa sashi na 97, 100 da 197 (a) na dokar hana aikata laifuka ta Criminal Procedure Code.

Sai dai lauyan wadanda ake zargi Yunusa Umar ya ce yawancinsu dalibai ne kuma an tsare su ne ba bisa ka'ida ba, domin sun haura sa'o'i 24 a hannun hukuma.

Daga nan sai alkalin kotun ya bayar da belinsu, inda za a ci gaba da shari'a a ranar 8 ga watan Mayu.

An dai haramta luwadi da madugo a Najeriya, kuma ana matukar kyamar masu aikata hakan.

Sai dai wannan ba shi ne karo na farko da ake tuhumar mutane da zargin aikata hakan ba.

Labarai masu alaka