An haramta amfani da danjar mota a Indiya

Mota mai dauke danja Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sau da yawa manyan jami'ai suna amfani da danjar don nuna matsayinsu.

Kasar Indiya za ta haramtawa Ministoci da manyan jami'an gwamnati amfani da fitilar danja a jikin motocinsu don hana su gudu a wurin tsayar da motoci.

Ministan kudin kasar Arun Jaitley ya ce, daga daya ga watan Mayu "babu wata mota da za a bari da jar danja,ko ta wacece"

A karkashin sabuwar dokar, motocin bayar da agaji,da motocin asibiti,da na kashe gobara ,da motocin jami'an tsaro ne kawai za su iya amfani da danjar.

Masu suka sun ce, sau da yawa manyan jami'an suna amfani da danjar a matsayin wata sheda da take nuna matsayinsu, inda hakan yake kawo hargitsi ga matafiya a wurin tsayar da motoci.

Har'ila yau ana zargin manyan 'yan siyasa da jami'an gwamnati da yin amfani da danjar domin su wuce wurin da ake tsayar da motoci a cikin gari idan suna gudanar da harkokin gwamnati don su nuna matsayinsu.

Mr. Jaitley ya ce, gwamnati za ta janye dokar da ta ba wa gwamnatin tarayya da ta jiha damar bayyana wanda zai iya amfani da danja.

Wakilan kafafen yada labarai sun ce matakin gwamnatin ya zo ne domin dakatar da dadaddiyar "al'adar kasar Indiya" ta dabi'ar manyan jami'ai da yake nuna 'yancin 'yan siyasa da manyan jami'an gwamnati sama da na talakawa.

Firai ministan kasar Narendra Modi, ya saka batun a shafin twitter don ya ji ta bakin masu bibiyarsa game da shawarar da gwamnatin nasa ta yanke.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito jawabin Ministan sufuri Nitin Gadkari , inda yake cewa,"Wata babbar shawara ce ta siyasa".

Ministan Delhi, babban birnin Indiya Arvind Kejriwal, ya tabbatar da cewa ba shi da danja a jikin motar shi, a lokacin da ya yi shugabanci a shekarar 2015.

A shekarar 2013, kotun kolin kasar Indiya ta ce, wadanda suke rike da ofishin tsarin mulki da suka hada da, shugaban kasa, da Fira minista, da ministoci, da manyan alkalai, da kuma wasu manyan jami'ai ne suke da damar saka danja a motocinsu.

Labarai masu alaka