Ana karbar Akuya a matsayin kudin Makaranta a Zimbabwe

Akuya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana karbar Akuya a matsayin kudin makaranta a Zimbabwe

Wani Ministan Gwamnatin kasar Zimbabwe ya ce, an bai wa Iyayen da ba za su iya biyawa 'ya'yansu kudin makaranta ba a kasar, damar bayar da dabbobi kamar awaki da tumaki a matsayin kudin makaranta.

Ministan ilimin kasar, Lazarus Dokora ne ya shaidawa wani Kamfanin jarida mai goyon bayan gwamnati cewa, yakamata makarantu su rika nuna sassauci a duk lokacin da suka bukaci karbar kudin makaranta daga hannun iyayen yara

Ministan ya ce ba iya dabbobi kawai za su rika karba ba , har ma da yin aiki ga wadanda suke da kwarewa a wani fanni." Misali idan an samu wanda ya iya yin gini a cikin jama'a mace ko namiji to dole ne su yi amfani da wannan damar su yi aikin a madadin biyan kudin makarantar.

Jaridar ta bayar da rahoton cewa, wadansu makarantun tuni suka fara karbar dabbobi a matsayin kudin makarantar.

Wani Jami'in ma'aikatar ya yi bayani kan ra'ayin Dr. Dokora da cewa,"Galibin iyayen da suke biyawa 'ya'yansu kudin makarantar ta hanyar amfani da dabbobi mazauna yankunan karkara ne, amma wadanda iyayensu suke zaune a birane da cikin gari suna biya ta wasu hanyoyin, misali yin wasu ayyukan a makaranta"

BBC ta kawo rahoton cewa, a makon da ya gabata ne kasar Zimbabwe ta ba wa mutane damar yin amfani da dabbobinsu, kamar Awaki,da Tumaki, da Shanu, wajen biyan bashin banki. A karkashin dokar da aka gabatarwa Majalisa a makon nan, an ba wa wadanda suka karbi bashin damar yin rijistar "kadarorin da za a iya daukarsu daga wani wuri zuwa wani wurin daban" wadanda suka hada da motoci da kayan aiki, a matsayin biyan kudin.

A cewar Kamfanin watsa labarai na Bulawyo24, kasar na fuskantar rikicin kudi wanda yake nuna cewa mutane na shafe sa'o'i suna bin layi a bankuna domin fitar da kudinsu. Gwamnati ta ce karancin kudin ya faru ne sakamakon yadda mutane suke daukar makudan kudade suna fitar wa daga kasar, sai dai masu suka sun ce hakan na faruwa ne sakamakon rashin zuba jari da kuma rashin aikin yi.