Wani jirgin saman Nigeria ya turnike da hayaki bayan ya tashi

Jirgin sama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hayaki ya turnuke jirgin ne mituna 20 bayan ya tashi

Jirgin saman mallakin Aero, ya turnuke da hayaki ne mituna 25 bayan ya tashi daga filin jirgin saman birnin Fatakwal dake jihar Rivers.

A lokacin da hayakin ya turnuke wasu daga cikin fasinjoji sun kasance cikin kwanciyar hankali yayinda wasu kuma suka rika rafka ihu suna adduo'i.

Daya daga cikin bidiyon da aka wallafa a shafin twitter na daya daga cikin mutanen da suke jirgin ya bayyana yadda abubuwa suka wakana.

Oriaku ta ce " mintuna 20 bayan jirginmu ya tashi, sai jirgin kamfanin Aero ya cika da hayaki. Sai da muka shafe mintuna 35 muna adduo'i wasu kuma suna ihu yayinda wasu kuma suka shiga rudani.

Ta kara da cewa ta shiga jirgin ne daga garin Fatakwal zuwa Legas a lokacin da jirgin ya turnuke da hayaki, kuma mutane suka fara adduo'i.

Oriaku ta ce " Matukin jirgin ya ce mu kwantar da hankalinmu amma dai wani abu yana konewa ga kuma warin abin da yake konewa sannan hayakin ya karu amma kuma duk da haka sai ya ce mu kwantar da hankalinmu".

Ta kuma ce amma jirgin ya sauka jihar Legas lafiya a daidai lokacin da ma'aikatan agaji ke jira domin su taiamaka.

Har yanzu dai ba a tabbatar da abin da ya haddasa hayakin ba kuma babu rahoton wani wanda ya jikkata.

Labarai masu alaka