Allah Ya yi wa Alhaji Ahmadu Chanchangi rasuwa

Ahmadu Chanchangi Hakkin mallakar hoto Family Members Facebook
Image caption Marigayin ya bar mata uku da 'ya'ya 33

Allah Ya yi wa fitaccen dan kasuwa kuma Shugaban kamfanin jiragen sama na Chanchangi Airlines a Najeriya Alhaji Ahmadu Chanchangi rasuwa.

Attajirin, wanda dan asalin Jihar Taraba ne, ya rasu ne a safiyar ranar Laraba a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, yayin da ake kokarin kai shi wani asibiti da ke Abuja.

Marigayin ya yi doguwar jinya gabanin rasuwarsa, kamar yadda wani na kusa da shi ya shaida wa BBC.

Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 33 cikinsu har da dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna Alhaji Rufa'i Chanchangi.

An yi jana'izarsa ne ranar Laraba a Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Mutuwar Alhaji Ahmadu Chanchangi ta tayar da hankulan mutane da dama a birnin Kaduna, sabo da abinda mutanen suke bayyanawa da irin taimakon da ya ke yi.

Hakkin mallakar hoto Family Member Facebook.
Image caption An yi jana'izar marigayin ne a gidansa da ke Kaduna ranar Laraba bayan sallar azahar
Image caption Daruruwan mutane dake alhini na tururwa zuwa gidan marigayi Chanchangi

Labarai masu alaka