Babachir: Ko Buhari ya fara sauya takunsa?

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dai dade ana cece-ku-ce kan Mista Babachir a kasar

Wasu masu sharhi na ganin cewa dakatar da sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar (NIA) Ambassador Ayo Oke da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na nuna yadda shugaban ya fara sauya takunsa.

Inda suka bayyana cewa an kara samun kwarin gwiwa a kan da yaki da cin hanci a kasar domin babban abin da yake jawo rashin kwarin gwiwa shi ne rashin tuhumar wadanda ke kusa da shugaban kasa,"

Wani dan jarida mai zaman kansa kuma mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a kasar Jaafar Jaafar ya ce "Idan ana yaki da cin hanci da rashawa kamata ya yi a hada kowa da kowa har da wadanda suke kusa da shugaban kasa , wato mambobin majalisar zartarwarsa da kuma ministoci."

"Matakin wani abu ne mai matukar muhimmanci kuma abu ne da ya yi wa al'ummar kasa dadi." In ji shi

Har ila yau, mai sharhin ya ce hakan na nuna cewa shugaban ya fara sauyawa daga yadda jama'a suke yi masa kallon wanda ya kasa daukar matakan da suka dace bayan hawansa mulki.

Daga nan ya yi magana kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke kasa samun nasara a mafi yawan shari'un da take yi a kotuna, bayan ta gurfanar da mutanen da take zargi.

Ya ce ya kamata gwamnati ta dukufa wajen mutunta dokokin yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar amfani da "diflomasiyya a wurin da ya dace".

Akwai kuma masu ganin cewa tun asali ma aikin Babachir da na daraktan NIA aiki ne da ya kamata a ce hukumar EFCC ce ke yinsu, ba majalisa ko kuma fadar shugaban kasa ba.

A watan Disamban bara ne wani rahoto da kwamitin majalisar dattawa ta fitar ya zargi Sakataren gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a karbar kwangilar "cire ciyawa" a wani sansanin 'yan gudun hijira, inda suka karbi makudan kudade ba tare da yin aikin da ya kamata ba.

Baya ga haka, 'yan majalisar sun yi zargin cewa Babachir Lawan ya sabawa ka'idojin aiki saboda ci gaba da zamansa shugaban kamfanin duk da cewa ya karbi mukamin sakataren gwamnatin tarayya.

Kwamitin majalisar wanda ya binciki batun zargin karkatar da kudaden, ya bukaci shugaba Buhari ya kori Babachir.

Labarai masu alaka