Buhari ya dakatar da Babachir da shugaban NIA

Babachir Lawal Hakkin mallakar hoto Other

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawan da darakta Janar na hukumar leken asirin Nigeria NIA Ambassador Ayo Oke kan zargin almundahana da kudaden gwamnati.

An dakatar da Babachir ne saboda zargin saba ka'idojin bada kwangila karkashin shirin gwamnati na raya yankin arewa maso gabas wanda Boko Haram ta daidaita.

Shi kuwa Ambassador Oke ya gamu da fushin shugaban ne har sai an kammala bincike kan kudin da hukumar EFCC ta gano a Legas.

Rahotanni sun ce hukumar NIA ta ce kudaden, kimanin naira biliyan 13, nata ne, abin da ya haifar da rudani a kasar.

Kakakin shugaban Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari ya kuma bada umarnin gudanar da gagarumin bincike kan kudaden na Legas.

Binciken dai zai gano yadda hukumar ta NIA ta samu wadannan makudan kudade, kuma waye ya bada umarnin samar mata da kudin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon yadda EFCC ta gano kudin da ba ta taba gano irinsu ba

Sannan kuma za a binciki ko an saba dokoki, ko kuma an keta matakan tsaro wajen neman inda aka ajiye kudin, da kuma hanyar da aka shirya amfani da su.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin binciken mai mutane uku.

Sauran mutanen sun hada da ministan shiri'ar kasar, Abubakar Malami, da mai bawa shugaban kasar shawara ta fuskar tsaro Babagana Munguno.

Ana sa ran za su mika sakamon binciken cikin mako biyu.

Sanarwar ta ce manyan sakatarori a ofishoshin mutanen da aka dakatar su ne za su rike mukaman a lokacin da ake binciken.

Labarai masu alaka

Karin bayani