Yadda ake zama gida daya da gawa

Wasu dauke da gawa
Image caption A wasu lokutan a kan sauya wa gawar tufafi sababbi har ma a zagaya kauyen da ita

A yankin Toraja da ke Sulawesi a kasar Indonesia, hakan ya zama tamkar wani bangare ne na rayuwarsu.

Gargadi: wasu masu karatu ba za su so kallon wasu daga cikin hotunan da ke cikin wannan labarin ba.

A cikin wani daki da ba kujeru, an saka hotuna, zaka ji muryoyin mutane da kuma kanshin gahawa. Wannan taro ne na iyali da sauran 'yan uwa.

Daya daga cikin bakin ya yi tambaya ''Ya lafiyar mahaifinka'', sai yanayin kowa ya sauya. Kowa ya kalli wani karamin daki da wani tsoho ke kwance a kan gado da aka yi wa ado.

'Yar sa Mamak Lisa ta amsa da cewa ''Har yanzu yana fama da rashin lafiya.''

Cikin murmushi, Mamak Lisa ta tafi kusa da tsohon, ta girgiza shi ta ce'' Mahaifina mun yi baki da suka zo duba ka. Ina fatan wannan ba zai bata maka rai ba.''

Sai ta kira ni na fito waje domin na ga Paulo Cirinda.

Na yi ta kallon gadon, Paulo Cirinda baya motsi ko da yake da wuya ka ga idanunsa.

Ko'ina a fatarsa ramuka ne kamar kwari sun cinye. Tufafin da aka sa masa ya rufe sauran jikinsa.

Na kura masa ido har sai da jikokinsa da ke wasa, suka shigo dakin sannan na dauke ido na.

Daya daga cikinsu ya ce ''Me ya sa kaka barci kullum''. Dayan kuma ya ce ''Kaka, tashi mu ci abinci.''

Mamak Lisa ta ce Shhh.. ''Kada ku damu kaka, yana barci. Zaku sa ya yi fushi.''

Abin mamaki shi ne, Paulo Cirinda, ya mutu fiye da shekara 12 da suka gabata, amma iyalinsa sun yi amannan cewa har yanzu yana raye.

Ga wasu wannan al'ada ta rayuwa tare da gawa a cikin gida, ba abu ne da aka saba gani ba.

Image caption Sai dangin mamaci sun tara kudi kafin ayi makokinsa

Amma ga mutane fiye da miliyan daya da ke yankin Toraja a Sulawesi da ke gabashin Indonesia, wannan al'ada ce da ake yi fiye da shekaru 100.

Bayan mutum ya mutu zai iya daukar watanni, a wasu lokutan ma har tsawon shekaru kafin a yi makokinsa. Kafin sannan kuma, 'yan uwan mamacin su kan ajiye gawar a gida su cugaba da kula da ita tamkar mutum mara lafiya.

Ana kawo wa gawar abinci da lemu da sigari sau biyu a rana.

Ana yi musu wanka kuma ana yawaita sauya musu tufafi a kai a kai.

Ana kuma ajiye wa gawar fo a wani lungu a daki, a matsayin abin da zata yi ba haya a ciki.

Har ila yau, ba a taba barin mamacin ba tare da wani ba kuma a ko da yaushe fitulun dakin gawar suna kasancewa a kunne duk sanda gari ya yi duhu.

Dangin gawar sun yi amannan cewa idan har ba su bai wa gawar kulawar da ta dace ba, fatalwarta zata dawo ta rika basu tsoro.

A al'ada, ana shafa wa gawar wasu ganyayyaki domin a hana ta rubewa.

Amma a baya-bayan nan , ana yi wa gawar wata allura maimakon amfani da ganyayyakin da aka saba amfani da su a baya.

Sai dai sinadarin da ake yin allurar da ita tana janyo wani wari mai karfi a dakin.

A lokacin da take shafa kumatun mahaifinta, Mamak Lisa ta ce har yanzu akwai shakuwa mai karfi tsakaninsu.

"Duk da cewa mu kirista ne," 'yan uwansa kan ziyarce shi ko su kira ta wayar tarho su ji yadda mahaifina yake, saboda mun yi amanna yana jin duk abin da muke fada kuma yana tare da mu.

Wani abin mamaki shi ne, Lisa ta shaida min cewa kasancewar gawar mahaifinta a gida ya taimaka mata wajen alhinin mutuwarsa.

A lokacin da suke raye 'yan kabilar Torajan suna aiki matuka domin su tara dukiya. Amma maimakon su mori wannan arzikin da suka tara, sai dai a tara domin a yi gagarumin biki a lokacin da za a yi makokinsu.

Gawar Cirinda zai kasance tare da mu har sai lokacin da 'yan uwansa suka shirya rabuwa da shi. Gawar zata bar gidan bayan an kewaye kauyen da ita a lokacin wani gagarumin biki.

Image caption A al'adance ana shafa wa gawar wasu ganyayyaki domin hana ta rubewa

A ala'adar kabilar Torajan, a lokacin da ake bikin matuwa ne ruhin mamacin ke barin doron kasa kuma ya fara sabon rayuwa bayan mutuwa.

Sun kuma yi ammanar cewa Bauna ce ta ke tafiya da ruhin inda gawar za ta yi wata sabuwar rayuwa kuma wannan ne dalilin da yasa dangin mamacin ke yanka Bauna da yawa a matsayin sadaukarwa a gare shi domin ya samu saukin tafiya.

Kabilar Torajan na shafe tsawon rayuwarsu suna tanadin abin da za a kashe a lokacin yin wannan al'adar.

A daidai lokacin da suke jin cewa sun tara iya abin da ya kamata, sai su gayyato 'yan uwa da abokan arzki daga sassan duniya daban-daban.

Iya kudin mamaci a lokacin da yake raye iya shagalin da za a yi a lokacin da za a yi shagulgulan makokinsa.

Wakiliyar BBC ta halarci wajen makokin wani mutum da ake kira Dengen wanda ya mutu sama da shekara daya da ya gabata.

Dengen mutum ne mai karfin iko kuma attajiri ne a lokacin da yake a raye.

An shafe kwana hudu ana shagulgulan makokin, inda aka yanka Bauna 24 da daruruwan Aladu a matsayin sadaka.

Daga baya sai a rarraba naman ga bakin da suka halarcin makokin.

Dan ya shaida wa wakiliyar BBC cewa sun kashe dala 50,000 wanda ya fi kudaden shigarsu na shekara a lokacin da ake bikin makokin.

Wakilyar BBC ta yi mamaki matuka, kuma sai ta kwatanta wannan makoki da ake ta shan shagali da na mahaifinta. Ta ce a lokacin da suka yi na mahaifinta ba su yi wani gagarumin biki ba, 'yan uwanta na jiki ne kawai suka zo suka yi dan karamin taro a wani wuri mai duhu kuma babu hayaniya.

Image caption Duk bayan wasu 'yan shekaru, 'yan uwa na fito da makarar wadanda suka dade da mutuwa su bude saboda gawar ta sake ganawa da 'yan uwa

Ta kara da cewa idan ta kwatanta yadda suka yi na mahaifinta da yadda dangin Degen suka sha shagali sai ta ji ta shiga tashin hankali.

Bayan makoki sai kuma a binne mamaci.

Ba kasafai ake binne 'yan kabilar Torajan a kabari ba, ana binne su ne a manyan kaburburan dangi ko kuma a binne su a ciki ko wajen koguna saboda yanki ne mai cike da tsaunuka.

Bayan duk wasu 'yan shekaru, 'yan uwa na fito da makarar wadanda suka dade da mutuwa sai su bude saboda gawar ta sake ganawa da 'yan uwa.

A taron da suke kira ma''nene 'yan uwa da abokan arziki suna yi wa gawar tayin abinci da sigari sannan kuma su goge jikinta.

Baya ga haka kuma sai su tattaro gangar jikin gawar a dauki sabon hoto na dangi.

Andy Tandi Lolo, wani farfesan halayyar dan adam ne a Torajan, ya bayyana wannan al'ada a matsayin wata cigaba da zumunci tsakanin wadanda suke raye da kuma wadanda suka mutu.

"Bayan da na dawo daga coci ranar lahadi, sai na raka wasu mutane zuwa kauyen Torajan a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa wani gini da ba su da tagogi. Makabartar dangi ce.

Mata na ta addu'oi suna kuka a wani yanayi mai ban tausayi.

Image caption A kan ajiye wasu gawarwakin har tsawon sama da shekara 10 ba a binne su ba

Estersobon na daya daga cikin bakin da ke da kusanci da surukar Maria Solo wadda ta mutu.

Da zarar kowa ya dan samu lokaci da Maria kuma an dauki hotuna da ita, sai a nade ta a cikin lukkafani kamar an sauya mata tufafi.

A kauyuka da dama su kan sauya tufafin gawar da sababbi har ma a zagaya kauyen da ita.

Sai a baya-bayan nan wannan al'adar ta fara bacewa saboda sama da kashi 80 cikin 100 na 'yan kabilar Torajan ba su bin addinin Aluk to dolo sun koma kirista.

Sakamakon haka a hankali a hankali abubuwa na sauyawa.

Duk da haka kirista da masu addinin Aluk to dolo sun shafe tsawon lokaci suna zamantakewa.

Image caption A yanzu ana amfani da wani sinadari domin hana gawar wari da rubewa a kauyen

Andy Tandi Lolo ta ce tun lokacin da masu da'awar addinin kirista na kasar jamus suka isa garin kasa da shekaru 100 da suka gabata, sun yi kokarin su hana addinin da amannar da suka yi cewa duk wani abu da Allah ya hallita a doron kasa yana da ruhi.

A cikin shekarun 1950, duk da dai sun gane cewa idan har suna so 'yan Torajan su amince da sabon addininsu, dole ne su nuna nasu su kyale su su cigaba da addininsu.

A wasu wurare a duniya wannan al'adar ba abin mamaki ba ce.

Tunawa da mamata na daga cikin abin da da yawa daga cikin mutane ke yi. Sai dai kawai 'yan Torajan na amfani da wata hanyar ta daban wajen yin hakan.

Labarai masu alaka