Babachir ya gana da Osinbajo, Shugaban NIA ya kasa ganinshi

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farfesa Yemi Osinbajo

Sakatare gwamnatin tarayyar Najeriya, Babachir David Lawal, wanda aka dakatar daga mukaminsa ya gana da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwato cewa, ganawar na da nasaba ne da kwamitin binciken da gwamnati ta kafa kan zargin almundahanan da ake yi wa Mista Babachir.

A ranar Laraba ne dai gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Farfesa Yemi Osinbajo, domin gano gaskiyar zargin da aka yi wa Babachir na amfani da mukaminsa domin samun kudi ta hanyar da ba ta dace ba.

Amman Babachir ya ki ya yi magana da manema labarai bayan ganawar.

Manema labarai sun kuma ga dakataccen daraktan hukumar leken asiri ta kasar NIA, Ayo Oke, a kusa da ofishin mataimakin shugaban Najeriyar bayan Babachir ya tafi.

Da Mista Oke ya ga manema labarai, sai ya juya domin bin hanyar fita ta ofishin mataimakin shugaban kasar, amman jami'an tsaro suka hana shi wucewa.

Kokarinsa na ganawa da mataimakin shugaban kasar Najeriyar dai ya ci tura.

Hukumar ta NIA ta yi ikirarin cewa ita ce ke mallakar wasu makudan kudade dala miliyan 43 da aka bankado a wani bene a Legas.

Kwamitin binciken da gwamnatin Najeriya ta kafa dai ya hada da Farfesa Yemi Osinbajo da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Majo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami.