Yadda yaki da jahilci ke karfafa guiwar mata

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kasance mai gwagwarmaya kan ilmin mata a Liberia

Mata a Liberia sun tashi haiƙan wajen yaƙi da jahilci bayan yaƙin basasar shekara 14 da ƙasar ta yi fama da shi ya sanya ɗumibin yara kauracewa makaranta baya ga karuwar mata marasa ilimi.

Kamar yawancin kasashen da suka fuskanci yaki, karatun yara ya samu koma-baya a Liberia, inda wasu daga ciki suka gaza ci gaba da makaranta.

Hukumomin Liberia da ƙungiyoyin ba da agaji sun ɓullo da wani shirin ilmantar da mata kyauta a kasar, inda ake fara karatu da yamma, hakan na bai wa matan damar gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Matan dai na bayar da himma a irin karatun da suke koyo, sukan yi wa juna bitar karatun da aka koya musu.

Wasu daga cikin dalibai matan da suke cin gajiyar shirin sun ce rayuwa ta sauya matuka tun da za su iya karatu da rubutu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matan dai a Liberia da dama sun lashi takobin neman ilmi a kasar

Victoria mai shekaru 41 ta shaida wa BBC cewa iyayenta ba su saka ta a makaranta ba, iya tsawon rayuwarta tana da kokarin ganin ta iya karatu da rubutu, kuma tana ganin alamar nasara.

Ta kuma ce '' Yanzu da na samu dama na mai da hankalina kan karatun, don ina son karatu matuka.''

Shirin da kungiyar Alfatlit ke jagoranta na yaki da jahuilci na da dalibai sama da dubu biyu kuma kashi 95 cikin dari na daliban mata ne.

Shugabar kungiyar Evelyn Kafada Segep ta shaida wa BBC cewa dalilan da suka sa mata suka fi yawa ba su wuce cewa mata ne suka fi fuskantar matsala wajen samun illmi, a tsakanin shekara 1950 zuwa 1960 ba.

Kuma iyaye sun fi sanya 'yayansu maza a makaranta fiye da mata, wannan ta sa an mata da dama a baya.

Tun a shekara ta 2006 ne, Shugaba Ellen Johnson Sirleaf take jagorantar Liberia, kuma ta kasance mai gwagwarmaya kan ilimin mata da horas da su yadda za su tsaya da kafafunsu ta hanyar sana'o'i da sauransu.

Hakan ya sa an samu karuwar makarantu ciki har da wadanda kungiyoyin kasasahen duniya ke jagoranta kamar Alfatlit.