Da gaske ne EFCC ta gano kudi a makabarta?

EFCC Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption An wallafa hoton ne bayan Lai Mohammed ya ce barayin gwamnati suna boye kudi a makabarta

A farkon makon nan ne Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya ce barayin gwamnati na boye kudi "a rami a cikin gidajensu da kuma cikin surkukin daji har ma da makabartu."

Tun bayan kalamansa ne aka fara yada wani hoto a kafafen sada zumunta a Najeriya, wanda yake nuna wata makabarta da jami'an hukumar EFCC suka kai samame don binciken wasu kudi da ake zargin an boye a ciki.

Ko hukumar EFCC ce ta wallafa hoton?

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya shaida wa BBC cewa "A'a, hoton ba daga wurinmu ya fito ba. Kuma ba mu taba yin samame a cikin makabarta ba."

Mene ne asali ko tushen wannan hoton bogen?

BBC ta gano asalin hoton, bayan ta bi sawunsa ta wasu hanyoyi daban-daban.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption EFCC tana ci gaba da farautar wadanda ake zargi da yin almundahana a kasar

Wasu ne wadanda da wuya a iya tantance ko su waye suka hada wasu hotuna biyu: daya na wasu jami'an hukumar EFCC, wanda aka dauko daga shafin Facebook din hukumar.

Hoto na biyu kuma an dauko shi ne daga shafin intanet din jaridar The Sun Daily ta kasar Malesiya, wanda yake nuna wasu mutane da su kai ziyara wata makabarta.

Hakkin mallakar hoto THE SUN DAILY
Image caption Nan kabarin wani dan Najeriya ne da ya mutu a Malesiya a shekarar 2014

Daga nan ne sai aka yanko hoton jikin jami'an EFCC aka jona shi da hoton makabartar wadda take garin Batu Arang a kasar Malesiya, kamar yadda bincike ya nuna.

Galibi a kan yi siddabaru da hotuna ne ta amfani da manhajar Photoshop.

Sai dai galibin masu mu'amala da kafafen sada zumunta a kasar ba su fahimci hakan ba, saboda sun ta yada hoton bogen da kuma bayyana ra'ayoyinsu game da abin da yake ikirarin nunawa, kamar haka:

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Jama'a sun ta bayyana ra'ayoyinsu game da hoton bogen

Labarai masu alaka