Matar da ta shiga ɗimuwa bayan da mijinta ya ɓata

Isatu Kanyi matar da mijinta ya bata
Image caption An bude kofifin amma banga mijina ba

A lokacin da shugaban Gambia, Adama Barrow ya karbi mulkin kasar daga hannun Yahya Jammeh 'yan kasar ke da buri. Amma watanni uku bayan an rantsar da shi, wakilin BBC, Umaru Fofana ya gano cewar mutane sun fara fitar da rai.

Kwanaki kadan kafin Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben da Adama ya yi nasara, mutanen da ke gidan kurkukun suka fara raguwa.

Iyalai da dama sun sake haduwa, wanda alama ce da ke nuna cewa an kawo karshen takurawa rayuwar mutane da kuma keta hakkin bil adama da aka yi a cikin shekaru 22 na mulkin Jammeh.

Duk da dai cewa a yanzu babu fursunonin siyasa a Gambia, amma ga Isatu Kanyi tana bukatar a wayar mata da kai kan lamarin da ke damunta.

A lokacin da ta ji cewa gwamnati za ta saki fursunonin siyasa, Misis Kanyi ta je kofar shiga gidan yarin Mile 2 da fatan za ta ga mijinta Kanyiba yana fitowa daga ciki.

Ta shaida wa BBC cewa an bude kofofin, mutane da dama sun rungumi masoyansu wadanda suka fito, amma ba ta ga mijinta ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Gambia da dama sun bazama a Titunan kasar domin murna bayan da aka sanar cewa Mista Barrow ne ya lashe zaben da aka gudanar a Disamba

Kanyiba Kanyi na daya daga cikin daruruwan mutanen da jami'an tsaro na hukumar leken asirin kasar ta kama.

An tsare su kuma a watan Satumbar shekarar 2006 aka kai shi gidan yarin Mile 2, inda ake tsare tare da azabbatar da fursunonin siyasa.

"Na sa ran zan sake ganinsa," kamar yadda matarsa ta ce.

Ta kara da cewa danta yakan tambaye ta inda mahaifinsa yake, ba abin da nake iya gaya masa sai dai na ce masa babanka ya yi tafiya.

An sauya wa hukumar da ke leken asiri ta kasar suna, kuma akwai shirin da ake yi na kwace ta baki daya. Ana tuhumar tsohon shugaban da wasu manyan jami'an hukumar da laifin azabtar da wani dan rajin kare dimokradiyya a bara.

Hakkin mallakar hoto RTS
Image caption Adama Barrow na gudun hijira a Senegal lokacin da aka rantsar da shi

A watan Janairu, shugabannin yammacin Afurka suka kai zababben shugaba Adama Barrow makwabciyar kasar Senegal.

A ranar 19 ga watan Janairu aka rantsar da shi a ofishin jakadancin Gambia da ke Dakar, babban birnin Senegal.

A yanzu 'yan kasar na jin cewa sun fi samun 'yanci. A kasar da za a iya kama mutum kawai saboda ya sanya rigar da ke dauke da rubutun da ke kira da a yi dimokradiyya.

Duk da haka, matasan Gambia, wadanda ke kan gaba a tabbatar da nasarar Mista Barrow, a yanzu suna cikin kunci kuma suna bayyana hakan a kafafen sada zumunta da muhawara irinsu facebook.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kasar Gambia suna jin cewa sun fi 'yanci a yanzu

"Gambia na kuka saboda tana bukatar abubuwa da dama- dole a duba harkar wutar lantarki, da kuma ruwa, kamar yadda wata matashiya ta fada a wata kasuwa da ke garin Serekunda, wanda shi ne gari mafi girma a kasar.

Mutane da dama na da irin wannan ra'ayin nata. Wasu kuwa batun aikin yi suke yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An rubuta maudu'in Gambia ta yanke shawara a jikin wani mutum-mutumi

A lokacin da Mista Jammeh ya dage kan cewa ba zai sauka daga kan mulki ba bayan zabe, ya kare wani katon kyalle da aka rubuta "'yan Gambia sun yanke shawara" da aka kafa a kan hanyar zuwa Banjul babban birnin kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya akan kama 'yan Gambia saboda sun saka rigar da aka yi rubutun da ke kira ga Demokuradiyya

Kyallayen wadanda aka bayyanasu bayan zaben, wata alama ce ta turjiya daga matasan Gambia.

Duk da haka, a yanzu wasu na gargadin za su fara lalata kyallayen da suka kare a baya idan har sabuwar gwamnatin ta ki gudanar da harkokin kasar yadda ya kamata.

Labarai masu alaka