Iran tana tsokane mana ido - Amurka

Men work inside a uranium conversion facility outside Isfahan (30 March 2005) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarjejeniyar ta kafa wa shirin samar da makamin nukiliyan Iran wasu iyakoki

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Rex Tillerson, ya zargi kasar Iran da cigaba da tsokana da neman tabarbarewar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma yi wa muradun Amurka zagon kasa a yankin.

Mista Tillerson ya ce: "Idan ba a taka wa Iran birki ba, tana iya kasancewa kamar Korea ta Arewa ta kuma sa duniya ta bi ta."

A baya-bayan nan Shugaba Donald Trump ya ba da umurnin cewar a sake duba yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da Iran.

Duk da haka Amurkan ta amince cewar Tehran tana mutunta yarjejeniyar ta shekarar 2015.

Kawo yanzu Iran ba ta yi wata magana a fili ba game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan.

Iran ta nace cewa zarge-zargen da kasashen yamma ke mata cewar tana kokarin hada makamin nukiliya ba gaskiya ba ne.

Me Amurka ta ke yi game da Iran?

A ranar Talata Amurka ta zargi Korea ta Arewa da neman "tsokano wani abu" bayan da ta gudanar da wani gwajin makami mai linzami wanda bai yi nasara ba a karshen mako.

Korea ta Arewa ta ce za ta iya gwajin makami mai linzami a kowane mako inda ta yi gargadin fara cikakken yaki idan har Amurka ta dau matakin soji a kanta.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 ta sa an dage wa Iran takunkumin da aka lankaya mata

Rex Tillerson ya ce manufar sake nazari kan yarjejeniyar, wanda ya riga ya sanar da majalisar dokokin Amurka, ita ce duba manufofin Amurka ga Iran wadda za ta kunshi yanayin yadda Iran take mutunta yarjejeniyar nukiliyar da kuma abubuwan da ta ke yi a Gabas ta Tsakiya.

Ya zargi kasar da "tayar da zaune tsaye da yada ta'addanci da kuma tashin hankali".

Mista Tillerson ya ce: "Iran ita ce kasar da ta fi tallawa ta'addanci a duniya kuma ita take zafafa tashe-tashen hankula da kuma yi wa muradun Amurka zagon kasa a kasashe irin su Siriya da Iraki da kuma Lebanon."

Ya soki rawar da Iran ke takawa a rikicin Siriya da kuma goyon bayan da ta ke bai wa Shugaba Bashar Al-Assad.

Labarai masu alaka