Nigeria: An kai samame gidan Sanata Danjuma Goje a Abuja

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba dai tabbatar da wanda ya ba da umurnin binciken da jami'an tsaron ke yi ba

A Najeriya jami'an tsaro sun kai same gidan tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje.

Sanata Goje ya tabbatar wa BBC binciken da jami'an 'yan sanda ke yi daki-daki a gidansa dake unguwar Asokoro, a babban birnin tarayyar kasar, Abuja, da yammacin Alhamis.

Sanata Goje mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya ya ce bai san dalilin binciken ba, kuma ba a bashi takardar sammaci ba gabanin binciken.

Danjuma Goje ya mulki jihar Gombe tsawon shekar takwas.