'Abin makalawa kan kwayar ido na karfin gani ya makanta ni'

Irenie Ekkeshis Hakkin mallakar hoto New Citizenship Project
Image caption Da fari ta yi tunanin kaikayi ne kawai idanun ke yi, ashe matsala ce gagaruma.

A lokacin da idanun Irenie Ekkeshis su ka fara kaikayi, sai ta yi zaton za su daina. A hankali sai radadin da idon ke yi ya karu, kafin aje ko ina ta rasa gani da ido daya. kuma ba wani abu ne ya janyo ma ta wannan matsala ba face daukar abin kara karfin gani da ake dorawa akan zinariyar ido da hannun ta jike da ruwa.

Da safiyar wata asabar, a watan Junairun shekarar 2011, Irenie Ekkeshis ta farka daga bacci idonta daya ya na hawaye, ba ta bata lokaci ba ta tafi wani shagon saida magani ta sayi wasu magungunan digawa a ido.

''Na yi tsammanin dan ciwon ido ne da mutum kan yi yau da gobe, a tunanina zuwa ranar litinin idon zai washe. amma a wannan rana da yamma ko dakin girki na gagara zuwa, saboda hasken wutar lantarkin gidana ya min karfi, sannan idona na min radadi da zogi''.

Ba tare da bata lokaci ba Ekkeshis ta tafi wani asibitin ido mai suna Moorfield's Eye Hospital, kuma likitocin ido da ke asibitin sun bata wasu magunguna masu radadi da zafin gaske. ciki kuwa har da yade wani abu da ya taru a kwayar ido na amma ba yana ce ba.

"Abin akwai matukar zafi, saboda ana amfani da wata allura ne siririya wajen yade shi, duk da cewa sun yi amfani da maganin digawa a ido da ke hana radadi, amma fa na sha wuya''.

Cikin kwanaki kadan, likitoci su ka shaida mata ta samu wani nau'in ciwon ido da ruwan fanfo, ko ruwan rafi, ko ruwan teku, ko kuma na kwamin wanka ke haddasawa.

"Na yi matukar kaduwa da tsorata a lokacin da likitan ya shaida min haka, kuma a wannan lokacin tuni na daina gani da ido daya. Ina ganin launuka daban-daban amma fa daga hakan ba na kara ganin komai'' in ji ta.

A kowacce shekara irin wannan nau'i na ciwon ido, yana shafar kusan mutane 125 a Birtaniya, kuma yawancin mutanen sun kamu da ciwon ne sanadiyyar sanya abin kara karfin gani na kwayar ido.

"Bana yin ninkaya, ko wanka idan abin kara karfin ganin yana ido na, amma yanzu na gano cewa ko da hannunka ne ba ka wanke da kyau ba ko kuma ba ka goge da kyalle mai kyau ba, za ka iya sanun wannan matsala," in ji Ekkeshis .

Image caption Kusan kashi 85% cikin 100 mutanen da ke kamuwa da nau'in ciwon idon da ke damun Ekkeshis abin kara karfin gani ka haddasa su.

A lokacin da Ekkeshis ta cika shekara 12 ne, ta yanke shawarar sauya kwankwamemen gilashin idonta da dan abinda ake sanyawa kan kwayar idon.

Da ta cika shekara 30 kuwa, sai ta fara amfani da abin makalawa a idon da ake sauyawa a kowacce rana, idan ta cire sai dai ta jefar da shi, kuma ba ta taba samun matsala da shi ba.

Image caption Akan dauki ciwon ido a hannu idan ba a wanke shi da kyau ba ko tsanewa da kyalle mai kyau

Da fari an bai wa Ekkeshis maganin digawa a ido bayan kowacce sa'a daya. likitocin sun shaida ma ta za a dauki makwanni kafin idon ya warke.

Amma duk da hakan babu wani sauki da ta samu, na radadin da idon ke yi.

"A hankali sai ciwo da radadin da idon ke yi ya karu matuka, a wasu lokutan na kan rasa inda zan sanya kai na na ji dadi, duk kuwa da maganin kashe radadin ciwo masu karfin gaske da likita ya bani.'' Inji ta.

A hankali sai ta gagara zuwa aiki, daga bisani babu yadda ta iya face ta ajiye aikin baki daya.

Sai da aka yi watanni 4 sannan likitocin suka fara shawo kan matsalar, idon ya dan rage ciwo. Amma a lokacin tuni idonta daya ya daina gani.


Menene za a iya yi idan an sanya abin kara karfin gani na kan kwayar ido

Abubuwan da za a yi

  • A tabbatar an wanke hannu tare da tsane shi da kyalle mai tsafta kafin a taba abin sanyawa a idon.
  • A tabbatar an sanya abin idon kafin yin kwalliya.
  • A tabbatar an rufe idanu ruf a lokacin da ake fesa turare, ko wani abu da yake bin iksa.

Abubuwan da ba za a yi ba:

  • Kar a shiga kwamin wanka, ko ninkaya ko shiga rana idan ana sanye da abin kara ganin, amma za a iya amfani da bakin tabarau dan kariya.
  • A tabbatar an cire shi daga ido kafin yin wanka, sai dai idan za a matse ido ruf ba tare da an bude shi ba.
  • A tabbatar an jika abin kara ganin cikin ruwan da likitoci ke badawa a asibiti ko kuma a jika shi da miyau amma shi ma a tabbatar babu dandano a baki.

Inda aka samo bayanin: Loveyourlenses.com


A watan Mayun shekarar 2013 ne akai mata aikin ido, kuma da alama an yi nasara.

"Abin farin ciki ne bayan tsahon lokaci da na dauka ba na gani da idona, ace yau ina iya gani da dukkan idanuna.'' Ta fada cikin annashuwa.

To amma fa, bayan kwanaki 10, sai Ekkeshis ta lura dayan idon na ta ya na mata hazo-hazo.

"Bayan binciken kwakwaf da aka yi, sai aka gano cewa ciwon ya sake dawowa kan inda aka min aikin, wato Ungulu ta koma gidanta na tsamiya.''

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Ciwon ya na sauyawa kwayar ido launi

An sake yi mata aikin ido a karo na biyu, a shekarar 2014.

"Idanuna sun gyaru, kuma na daina jin ciwo ko radadin nan da ya ke min a baya,'' inji ta.

Tsugune ba ta kare ba, dan kuwa ba da jimawa ba sai ta kara samun matsala a idon, abin da ya janyo baki daya idon ya daina gani. likitocin sun shaida mata cewa matsalar babba ce dan kuwa ta yadu kusan ko ina a idon sanadiyyar wancan ciwon ido na farko da ta fari yi. dan haka ba lallai ne ta kara gani da idon ba.

A lokacin da Ekkeshis ta ke jiyya, ta gano cewa babu wani a cikin kawaye ko 'yan uwa da abokan arziki da yawancinsu su na amfani da abin makalawa a kwayar ido dan kara karfin gani da suka san illar da bari ruwa ya taba shi ke haddasawa. Dan haka sai ta yanke shawarar za ta fara wani gangami dan wayar da kan masu amfani da abin ido sanin illar da wasu abuwa ke janyowa idan ana amfani da shi.

Ta kara gano, duk da a bayan kwalin abin sanyawa a idon na kunshe da gargadin yadda za a yi amfani da shi, ta lura ba a rubuta abubuwan da suke janyo nakasu ga ido ba idan aka kuskure wajen sanyawa a ido. Dan haka ne mutane ba sa fahimtar illolin kai tsaye.

Image caption Cibiyar kula da abin makalawa kan kwayar ido dan kara karfin gani ta Birtaniya ta samar da wata takarda da za a manna a bayan kwalin da aka rubuta ''Kada ku yi amfani da ruwa a jikin sa''

Ta kuma tambayi Cibiyar kula da abin makalawa kan kwayar ido dan kara karfin gani ta Birtaniya dalilin da ya sanya ba sa rubuta gargadin a bayan kwalin.

Ta kara da cewa "A wannan lokacin ne suka gane na dauki abin da muhimmanci, dan haka sai suka ba ni goyon baya. Muka fara lika gargadin a jikin kwalin.''

Ba a nan Ekkeshis tsaya ba, ta sha gabatar da jawabi a wuraren taro dan jama'a su san illar da ke cikin aikata abinda ya janyo ma ta makanta, ba Birtaniya kadai ba har ma da kasar Amurka.

Ta na kuma fatan, wata rana za a dinga makala gargadin hana amfani da ruwa a jikin dukkan kwalayen abin kara karfin ganin da za a samar kuma ya amfani al'umar duniya baki daya.