Kun san magajiyar sakataren gwamnatin Nigeria Babachir?

Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya nada magajin Babachir

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya nada Dr. Habibat Lawal a matsayin mai rikon mukamin sakataren gwamnatin kasar.

Haka kuma shugaban ya nada Ambasada Arab Yadman a matsayin mai rikon mukamin shugaban hukumar leken asiri ta kasar NIA.

Ambasada Arab Yadam dai shi ne mafi girman mukami a ofishin hukumar ta leken asirin, sannan Dr Habibat kuma ita ce mafi girman mukami a tsakanin manyan sakatarorin da ke ofishin sakataren gwamnatin na Nigeria.

A ranar Laraba ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawal, saboda zargin saba dokokin bayar da kwangila.

Haka kuma an dakatar da shugaban hukumar leken asirin kasar NIA Ayo Oke, saboda wasu makudan kudade da hukumar EFCC ta gano a wani gida a Lagos.

Shugaban Buhari dai ya nada mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin bincike mai mutane uku da za su mika rahotonsu a cikin mako biyu.

Sauran masu binciken su ne mai ba wa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Babagana Mungono da kuma ministan shari'ar kasar Abubakar Malami.

Labarai masu alaka

Karin bayani