Mutum biyu sun mutu a wani hari da aka kai birnin Paris

Birnin Paris Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani jami'in dan sanda ya toshe hanyar da ke kai wa ga inda aka kai harin a Champs Elysees

Wani hari da aka kai kan motar 'yan sanda a birnin Paris na ƙasar Faransa ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda guda, wasu biyu kuma sun samu munanan raunuka, a titin Champs Elysees.

Yan sanda sun harbe ɗan bindigar wanda ya fito daga cikin mota kafin ya fara ɓarin wuta da bindiga mai sarrafa kanta.

Ma'aikatar harkokin cikin gida a ƙasar Faransar ta ce tana da yaƙinin cewa da niyya aka kai wa jami'an 'yan sandan hari.

Hukumar yaki da ta'addanci ta fara gudanar da bincike, yayin da wasu rahotannin kafofin yaɗa labarai a yankin suka ce ɗan bindigar sananne ne a wajen hukumar leƙen asirin Faransa.

Harin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin gudanar da zagayen farko na zaben shugaban ƙasa.

Har yanzu dokar ta-ɓacin da aka kafa na aiki a ƙasar, tun bayan wasu kashe-kashe da masu kaifin kishin addini suka yi a birnin Paris cikin shekara ta 2015.

An girke jami'an tsaro dubu hamsin domin zaɓen da za a gudanar ranar Lahadi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Hollande ya ce yana da yakinin harin na da alaka da ayyukan ta'addanci

Shugaban Faransa Francois Hollande ya shaida wa manema labari cewa yana da yaƙini wannan hari yana da alaka da ayyukan ta'addanci.

Mr Hollande ya ce zai gana da manyan jami'an tsaron gwamnatinsa da safiyar Juma'a, don ɗaukar matakan da suka dace.

"Dakarun tsaronmu, da jami'an 'yan sandanmu za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana. Za kuma mu ci gaba da sa ido musammam a daidai lokacin da zabe ke daɗa ƙaratowa.'' in ji Hollande.''

Dubban sojoji da 'yan sanda ne ke gadin wuraren yawon bude ido a Paris babban birnin kasar ta Faransa.

Labarai masu alaka