An kama malamin da ya tsere da ɗalibarsa

Tennessee Teacher Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An taɓa ganin malamin da ɗalibar na sumbatar juna a aji

An kama wani malami daga jihar Tennessee ta Amurka bayan an zarge shi da sace ɗalibarsa 'yar shekara 15 a wani wuri mai nisan kilomita dubbai.

Ofishin binciken laifuka na Tennessee ya ba da sanarwar cewa an kama Tad Cummins a arewacin California.

Malamin da ɗalibarsa, sun ɓata tsawon wata ɗaya kafin a same su a kusa da dajin Shasta-Trinity mai tazara, a cewar wata jaridar Tennessee.

Mai gidan da aka gano motar malamin, ya ce Mista Cummins yana neman aiki a yankin.

Wani lauyan iyayen ɗalibar ya ce: "Babu kalmomi a harshen Ingilishi da za su iya zayyana irin daɗi da shauƙin da iyalan Thomas ke ji."

Hakkin mallakar hoto TBI
Image caption An shafe tsawon wata ɗaya ana nema kafin a kama malamin a arewacin California

Jason Whatley ya ƙara da cewa: "An shiga wata rayuwa mai wuya, amma a yanzu dai, murna muke yi."

Ɗalibar ba ta gana da iyayenta ba tukunna saboda tana can nesa a inda take, sai da 'yan sanda suka yi tattaki cikin ƙanƙara kafin su kamo malamin, in ji lauya.

Mista Cummins mai shekara 50 malamin Elizabeth a makarantar Culleoka Unit da ke yankin Maury County a jihar Tennessee.

Jami'an Tennessee sun ce "mai yiwuwa ya tozarta matsayinsa na malami, da ya rabo wannan ƙaramar yarinya da iyayenta tsawon wani lokaci a ƙoƙarinsa na lasa mata zuma a baki da kuma ƙila yin lalata da ita".

A rana 13 ga watan jiya aka neme su aka rasa, makwanni bayan wani ɗalibi ya gan su suna sumbatar juna a cikin aji.

Hakkin mallakar hoto TBI
Image caption An ga mutanen biyu suna giftawa a bidiyon sirri na Walmart

An ga giftawarsu a kyamarorin sirri da ke Walmart a birnin Oklahoma, daga nan kuma ba a sake jin ɗuriyarsu ba.

An dakatar da Mista Cummins daga koyarwa a watan Fabrairu bayan ya gaza bin umarnin shugabannin makarantar na cewa ya fita daga harkar wannan matashiya.

Hukumomi sun ce kafin ya tsere, sai da Mista Cummins ya gudanar da bincike a intanet kan "auren yarinya".

Ya kuma sayi abin canza launin gashi, kuma ya ci bashin dala 4,500, tare da gudanar da bincike a kan ko ana iya bin sawun motarsa Nissan Rogue, a cewar jami'ai.

'Yan sanda suna ɗaukar Mista Cummins a matsayin wanda ke ɗauke da makamai kuma mutum mai hatsari a lokacin da suke farautarsa.

A cewar wata takardar ƙorafi da iyayen yarinyar suka shigar gaban kotu a farkon wannan wata, Mista Cummins "cikin hikima ya riƙa shirya wa matashiyar gadar zare" inda ya tilasta mata fita tare da shi ta hanyar yi mata barazanar cewa za ta gamu da sakayya a makaranta idan ta ƙi.

Bayanan takardun ƙara sun ce Mista Cummins - wanda ya yi aure shekara 31 a baya - ya riƙa ziyartar yarinyar a gida, inda yake fita da ita ci abinci, yana ma zuwa gidan abincin da take aiki.

"Yarinyar ta riƙa faɗa wa 'yan'uwanta da ƙawayenta cewa tana tsoron malamin nasu," in ji takardun ƙara.

Matar malamin, Jill Cummins dai ta shigar da buƙatar neman a raba aurensu, a daidai lokacin da jami'ai ke ƙoƙarin kama shi.

Ta faɗa wa kafar yaɗa labarai ta ABC News cewa: "Son kai ya yi masa yawa."

"Ina son shi, amma na daina amincewa da shi. Gaba ɗaya ya ci amanata."