Nigeria: Lantarki ya kashe 'yan kallon wasan Man United

Gidan kallon kwallo a Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gidajen kallo na da farin jini sosai a Najeriya

Wutar lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wani gidan kallon kwallon kafa a garin Calabar na Jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya kirga gawarwakin mutum 16, yayin da wasu rahotanni ke cewa wadanda suka mutu sun haura 30.

Amma mai magana da yawun 'yan sandan Cross River, Irene Ugbo, ta shaida wa BBC cewa kawo yanzu mutum bakwai ne suka mutu yayin da 10 suke asibiti.

Lamarin ya faru lokacin da jama'a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch ranar Alhamis da daddare.

A sakon da ya aike na ta'aziyya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kadu kwarai da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Wata sanarwa da mai magana yawunsa Garba Shehu ya fitar ta ce shugaban ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma jama'ar jihar Cross River, sannan da masoya kwallon kafa a duk fadin Najeria.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Manchester United ya bayyana alhininsa ga 'yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Hakkin mallakar hoto Manchester United

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama'a.

Anthony Sunday ya ce "Ni da kaina na kirga gawarwaki sun kai 16, kuma jama'ar da ke wurin sun gaya min cewa adadin zai haura 31".

Mista Sunday ya kara da cewa jim kadan bayan lamarin sai wurin ya rikide inda jama'a suka rinka gudu domin neman mafita.

An rinka zuba gawarwaki da wadanda suka samu raunuka a motar 'yan sanda, in ji shi.

'Da karfe 10 abin ya faru'

'Yan sanda sun ce an garzaya da wadanda suka samu rauni asibiti domin yi musu magani.

Manchester United ce dai ta samu nasara a wasan da ci 2-1 wato 3-2 jumulla bayan wasa biyu, inda ta kai zagayen daf da na karshe a gasar ta Europa League.

Irene Ugbo ta ce da misalin karfe 10 na dare ne aka shaida wa 'yan sanda cewa lamarin ya faru kuma nan take jami'ansu suka bazama wurin.

Ta kara da cewa "bayanan da muka samu sun nuna cewa babbar wayar wutar, wacce ke kusa da gidan kallon, ta fado ne kan ginin".

Gini a hanyar da irin wadannan layukan wutar suka bi dai ya saba wa doka a Najeriya.

Sai dai ba kasafai ake daukar matakin hana mutane yin gine-gine a kusa da su ba.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Manchester United ta doke Anderlecht da ci 2-1 a ranar Alhamis wato 3-2 jumulla bayan wasa biyu

Labarai masu alaka