An hana Ahmadinejad tsayawa takarar shugabancin Iran

IRAN Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ahmadinejad (daga hagu) ya bijire wa Shugaban Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, inda ya cike takardun tsayawa takara a makon jiya

Hukumar da ke tantance 'yan takara a zaben Iran ta hana tsohon shugaban Kasar Mahmoud Ahmadinejad damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta bayyana.

Ahmadinejad, wanda mutum ne mai sukar kasashen yamma, ya mulki kasar karo biyu tsakanin shekarar 2005 zuwa 2013.

A makon jiya ne Ahmadinejad, ya cike takardar tsayawa takara a zaben, duk da gargadin da jagoran addinin kasar ya yi masa na kada ya yi hakan.

Sai dai hukumar - wadda mambobinta malamai ne - ta bai wa Shugaba Hassan Rouhani da kuma wani mai tsaurin ra'ayi Ebrahim Raisi damar tsayawa a zaben wanda za a yi a ranar 19 ga watan Mayu.

Hakazalika, an bai wa mataimakin shugaba kasar Eshaq Jahangiri damar tsayawa, sai dai kuma an hana Hamid Baghaie, wani na hannun damar Ahmadinejad, tsayawa.

A ranar Alhamis ne za a fitar da kammalallen sunayen 'yan takarar da su yi takara a zaben .

Fiye da 'yan takara 1,600 ne suke bayyana aniyyar tsayawa takara, sai dai kimanin shida ne hukumar ta baiwa damar tsayawa.

Bai wa Shugaba Rouhani da Mitsa Raisi damar fafatawa a zaben yana nuni da yadda za a fafata tsakanin bangarorin siyarar kasar biyu mabambanta.

Masu sharhi suna ganin Mista Raisi yana samun goyon bayan Shugaban Addinin Kasar Ayatollah Ali Khamenei.

Labarai masu alaka